MUN KAFA KUNGIYAR GBAKAKO DON SAMAR DA SHUGABANNIN DA ZASU RAYA YANKIN GABASHIN NEJA – Awaisu Wana
Daga Bala Musa Minna
An bayyana cewa kungiyar GBAKAKO wacce aka kafa don neman hadin kan al’ummar yankin gabashin jihar Neja ko ( Zone ‘B’ ) zata samar shugabannin da zasu kawo ci gaban da al’ummar yankin suke bukata
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Muhammadu Awaisu Giwa Wana, wanda shi ne uban kungiyar (grand patron) kuma jigo a jam’iyyar APC. Lokacin daya zanta da wakilinmu, a jiya Talata albarkacin ranar bukin ‘yancin Nijeriya
Inda ya ce ” shekaru ashirin da suka gabata nayi rajistar wannan kungiyar. Domin hadin kan kabilun Gwarawa ( Gbagyi ), Kadara, Koro, Ingwai, Kamuku, Urawa, Gwandara da sauran kabilu. Wadanda suke zaune a yankin gabashin jihar Neja saboda kawo ci gaban al’ummar dake ciki da wajen jihar
Ya ce ” kodayake akwai manyan ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, manoma da sauransu a a yankin, amma akwai bukatar samar da tsayayyun shugabanni a yankin masu kishin al’ummar gabashin Neja.
Don magance matsalolin rashin tsaro, lalacewar tattalin arziki, da sauransu wadanda suke janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al’ummar Gwarawa (Gbagyi) dana sauran kabilun wannan yankin
Har lia yau, Alhaji Awaisu Wana ya ce ” rashin gudanar da tsarin mulkin siyasa mai inganci yadda zai dace a mutanen Nijeriya ne wajen shugabanci, ya janyo wahalhalun da al’umma suke fama da su a halin yanzu a kasar nan
Inda ya ce ” idan za’a iya tunawa a shekaru hamsin da suka wuce, lokacin da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Sir, Ahmadu Bello da sauran ‘yan siyasa na farko a kasar nan suma mulki, al’umma ta anfana sosai daga wajen gwamnati giye da yanzu a kowane bangare
Amma yanzu, kowa yana fama da matsalolin tsadar rayuwa, talauci, rashin tsaro da sauransu a jihar Neja da kuma ko’ina a fadin Nijeriya.
Shi yasa muka kafa wannan kungiyar domin lalubo shugabannin da zasu hada kan al’umnar wannan yankin namu na gabashin Neja.Wadanda mafi yawansu manoma ne kuma suna kiwo da sauran ayyukan ci gaban rayuwarsu
Kuma su taimaka mana wajen magance sauran matsalolin da suke damun mutanenmu. Musamman wajen bunkasa rayuwar matasan dake bukatar ilmi da sana’o’in ci gaban al’umma
Haka nan Alhaji Awaisu Giwa ya kawo tarihin yadda lamarin gudanar da mulkin al’ummar Nijeriya bayan samun ‘yancin kai na Nijeriya ( independence ) daga hannun turawan Ingila yake a shekarar 1960.
Inda ya ce ” gaskiya bayan samun ‘yancin kai , shugabannin Nijeriya na wancan lokacin irinsu Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Sir, Ahmadu Bello da sauran shugabannin siyasa.dana mulki, sun taimakawa al’umma. Wajen ci gabanta fiye da wannan lokacin na yanzu
Ya ce ” shi yasa nake kira ga al’ummar yankin gabashin Neja dasu baiwa wannan kungiyar goyon bayan daya dace. Wajen samar da shugabannin da suke da kishin taimakawa mutanen wannan yankin. Domin bunkasa arzkinsu, ilmi da tsaron rayukansu mutanensu