SHUGABAN HUKUMAR KULA DA MAKARANTUN ISLAMIYYA NA NEJA YA NEMI GOYON BAYAN AL’UMMA
Daga Bala Musa Minna
Anyi kira ga malaman addinin musulunci, iyaye tare da sauran al’ummar jihar Neja, wajen baiwa hukumar kula da harkokin makarantun Islamiyya na jihar Neja ( NISIS ) goyon bayan daya dace. Domin samun nasarar ci gaban harkokin karatu a makarantun Islamiyya
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Ustaz Abdullahi Arab Yabagi, wanda shi ne shugaban hukumar kula da makarantun Islamiyya na jihar Neja, kuma shugaban makarantar Madarasatu Babul Islam dake Type ‘B’ Quarters, anan garin Minna
Lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake Progress Court, anan Minna, a jiya laraba
Inda ya ce ” ina kira ga malaman addini, iyaye tare da sauran masu ruwa da tsaki (stakeholders) a harkar kula da makarantun Islamiyya dake jihar Neja, dasu baiwa wannan hukuma ta kula da makarantun Islamiyya na Jihar, goyon bayan daya dace.
Saboda bunkasa fannin karatun da ake gudanarwa a makarantun Islamiyya a fadin jihar. Ta yadda zasu iya horas da ‘daliban da zasu iya anfanar da al’umma a fannonin ilmi . Musamman na addini da sauran harkokin rayuwa
Ya kara da cewa ” wannan shugabancin da nake yi a wannan hukuma ta NISIS, wanda gwamna manomi Rt. Hon Umar Muhammed Bago ya zabe ni akansa, yana nuna cewa ina wakiltar malaman makarantun Islamiyya ne dake fadin jihar.
Shi yasa nake kira ga malamai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki (stakeholders) a wannan bangaren. Wajen baiwa wannan hukuma goyon bayan daya kamata wajen samun nasara. Don ci gaban addini karkashin tsarin makarantun Islamiyya a jihar
Bugu da kari, shugaban ya ce ” wannan hukumar kula da makarantun Islamiyya na jihar, tana kokarin bunkasa ilmi da dabarun koyarwa na malaman wadannan makarantun a fannoni daban-daban, ciki har da koyar da sana’o’i ga malaman makarantun Islaniyya na jihar ”
Sai kuma kokarin samar da kyakkyawan alaka tsakanin hukumar da hukumar kulawa da malaman da suke koyar da harshen larabci a Nijeriya wato NATAIS. Domin samar da ingantaccen tsarin daya dace da zamani a wajen koyar da ilmin addini da harshen larabci ga ‘dalibai
Ya ce ” a cikin watanni takwas da kafa wannan hukuma mai kulawa da makarantun Islamiyya a jihar Neja, mun samu nasarar gudanar da ayyukan ci gaban makarantun Islamiyya daban-daban a fadin jihar
A karshe, Ustaz Abdullahi Arab ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Neja Rt. Hon Umar Bago, malaman addini da sauran masu taimakawa wannan hukumarsa wajen gudanar da ayyukansu a fadin jihar