ZAN BUNKASA MATASAN YANKIN CHANCHAGA – Hon Ibrahim Abdul-Azeez
Daga Bala Musa Minna
‘Dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Chachanga dake nan Jihar Neja na Jam’iyyar NNPP Hon Ibrahim Abdul- Azeez (The Eagle) yayi alkawarin bunkasa ci gaban matasan yankin Chanchaga
Hon Abdul-Azeez yayi wannan bayanin ne lokacin taron kaddamar da yankin neman zabensa. Wanda ya gudana a cibiyar raya al’adu ta U.K. Bello Arts Theatre dake nan Minna, ranar Laraba data gabata
Ya ce ” idan mutanen karamar hukumar Chanchaga suka zabe ni lokacin wannan zabe dake tafe na ‘yan majalisar wakilai na tarayya karkashin jam’iyyar NNPP, zan samar da tsarin bayanai na yanar gizo ( e- Data Base Information system)
Wanda yake dauke da bayanai na adadin mutanen mazabar Chanchaga, musamman matasan yankin. Don in samar da wuraren koyon sana’o’i da ilmin zamani da sauran su gare su. Domin samun zaman lafiya da tsaro a yankin
Zan yi wadannan ayyukan ne don magance matsalar rashin ayyukan yi dake damun al’umma. Wanda hakan yake janyo matasa suna shiga matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da aikata ta’addacin da matasan yankin suke yi ga Jama’a.
Bugu da kari Hon Ibrahim Abdul-Azeez ya ce ” idan nayi nasarar lashe wannan zaben, zan samar da tsarin kiwon lafiya kyauta ga mata da yara da mutanen da shekarunsu ya haura sittin da biyar. Don su rika anfana daga ayyukan gwamnati
Haka nan zan tallafawa kungiyoyin ‘yan kasuwa. Ta yadda zasu samu ci gaba a harkokin kasuwancinsu a cikin Jihar Neja da wasu wuraren. Don a magance dogara da ayyukan albashi na gwamnati
A karshe Hon Ibrahim Abdul-Azeez ya nemi mutanen mazabar Chanchaga dasu mallaki katin zabe na PVC don zabensa karkashin jam’iyyar NNPP a zaben dake tafe
Haka nan shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Neja Alhaji Mamman Damisa wanda ya karfafa Jam a’ar mazabar Chanchaga da Jihar Neja.
Wajen ganin sun zabi Jam’iyyar NNPP a zabubbukan dake tafe na bana. Saboda samar da canji na rayuwar mutane Neja da Nijeriya. Da magance matsaloln da al’umma suke fama dasu a yanzu karkashin gwamnatin APC