AN YI TARON KUNGIYAR HUFFAZUL QUR’AN & SCHOLARS
TA KASA A MINNA
Daga Bala Musa Minna
Kungiyar mahaddata Alkur’ani mai Girma da malaman addini ta kasa wacce ake kira Huffazul Qur’an & Scholars Association of Nigeria ta gudanar da taron ta na kasa a garin Minna na Jihar Neja,
Taron ya gudana ne a cibiyar Hon. Justice Idris Legbo Kutigi dake daura da gidan gwamnatin Jihar anan Minna.
Inda Alarammomi mahaddata kuma gwanayen karatun Alkur’ani mai Girma ‘ya’yan wannan kungiyar daga Jihohin Nijeriya guda 33 ne, suka halarci taron
Dayake gabatar da jawabinsa ga mahalarta taron, shugaban kungiyar Huffazul Qur’an & Islamic Scholars Association ta Nijeriya Gwani Aliyu Salihu Turaki kuma babban limamin masallacin Juma’a na Alhasan ‘Dantata dake Kano ya yi kira ga al’umma wajen raya karatun Alkur’ani mai Girma
Inda ya ce ” wajibi ne raya karatun Alkur’ani don muhimmancinsa ga al’umma. Musamman wajen ci gaban addini da harkokin yau da kullum. Saboda samun rahamar Allah Ta’ala anan duniya da lahira.
Shi yasa nake kiran gwamnatin tarayya da na Jihohin Nijeriya, dasu muhimmantar da lamarin karatun Alkur’ani mai Girma na allo.
Ta hanyar inganta tsarin karatun Tsangaya. Don ta wannan tsarin ne kadai ake haddace Alkur’ani da kiyaye shi yadda ya dace.
Saboda babban muhimmin aikin wannan kungiyar shi ne kokarin kare martabar Alkur’ani da masu karatunsa don ci gaban addini
Ya ce ” ya dace gwamnati ta samar da duk abubuwan da ake bukata a wannan bangaren don bunkasa karatun Alkur’ani. Yadda gwamnati take warewa bangaren ilmin boko miliyoyin kudade saboda ya bunkasa
Haka nan Farfesa Muhammad Nasiru Maiturare tsohon shugabann Jami’ar IBB dake Lapai a Jihar Neja ya bayyana muhimmancin wannan taro ne a yanu ga al’umma
Inda ya ce ” ana gudanar da ire-iren wadannan tarurrukan ne don wayar da kan mahadda alkr’ni kodon samar da tsarin karatun Tsagaya mai inganci. Kuma tsarin karatun Alkur’ani mai Girma na Tsangaya, yafi kowane tsarin karatu inganci.
Saboda muhimmancinsa wajen samar da karatun Alkur’ani ga almajirai yadda sukan haddace Alkur’ani har su iya rubuta shi da kansu yadda Allah Ta’ala ya saukar da shi . Shi yasa tsari ne mai inganci
Domin anan ne kadai ake baiwa kowane almajiri damar ya rika yin karatunsa da allonsa daidai da fahimtar sa da hazakarsa a makaranta. Har ya fahimci karatun ko ya haddace shi.
Ya ce ” ko turawa masu bincike na kasashen duniya da suka zo Nijeriya suka yi bincike akan tsarin karatun Alkur’ani na Tsangaya, sun tabbatar da cewa, yafi kowane tsarin karatu inganci sosai
Bugu da kari shugaban kungiyar Huffazul Qur’an ta Jihar Neja Ambasada Gwani Abubakar Sadik Maiturare ya ce ” wannan taro ne mai mubimmancin gaske ga Jihar Neja da Nijeriya.
Kodayake manyan kusoshin gwamnatin Jihar da muka gayyata basu halarci taron ba. Akwai bukatar gwamnatin Neja tayi koyi da gwamnatocin wasu Jihohin kasar nan.Wajen baiwa karatun Alkur’ani na allo muhimmancin daya dace
Kuma muna da kyakkayawan fatan za’a samar da mafita wajen ci gaba da inganta karatun tsangaya a karshen wannan taro na kasa da aka gudanar anan Minna na Jihar. Neja
Shi ma shugaban makarantun Tsangaya na zamani a Nijeriya Ambadasa Dakra Sa’idu Hasan ya ce ” ya kamata mahadda Alkur’ani suyi kokarin ganin martabar karatun Alkur’ani ya samu bunkasa
Domin binciken masana ya nuna cewa babu wata kasa a duniya da tafi Nijeriya yawan mahaddata Alkur’ani. Sai dai, ba’a girmamasu yadda ake yi a wasu kasashen musulmi na duniya
Ya ce ” muna kira ga ‘yan siyasa da al’ummar Nijeriya. dasu goyi bayan kuduri (bill) da ‘dan majalisa daga Jihar Sakkwato Hon Abdullahi Shehu Balarabe
Kakale ya gabatar gaban majalisar tarayya
Akan inganta tsarin karatun Alkur’ani ta hanyar Tsangaya domin muhimmanci sa ga al’umma. Da yadda za’a magance matsalar barace-barace na almajirai masu karatun Alkur’ani ta hanyar Allo
Kungiyar ta yaba da gudumnawar da Sarakunan Minna, Bida, Kagara da Agaie suke baiwa kungiyar don ci gabanta a Jihar Neja. Sannan kokarin samar da kyakkyawan alaka tsakanin gwamnati da ‘ya’yan kungiyar a fadin Jihar
A lokacin taron dai, an kafa wata gidauniya don samar da cibiyar da almajirai masu karatun Alkur’ani zasu rika zama suna karatun. Kuma cibiyar zata kunshi azuzuwan karatu, asibiti, wuraren koyon sana’o’i don anfanar da al’umma gaba daya
Haka nan kungiyar Huffazul Qur’an ta Jihar Neja karkashin shugabancin Ambasada Gwani Abubakar Maiturare ta baiwa almajirai sama da biyu kayayyakin sana’o’i don tallafa masu. Ta yadda zasu iya dogara da kansu. Kuma.su anfanar da al’umma
A karshe shugaban hukumar kula da harkokin addini.na Jihar Neja Shaikh Umar Beji ya yaba da wannan kokari na wannan. kungiyar. Musamman wajen ganin tana kokarin martabar Alkr’ani da mutanen dake karatun Alkur’ani.
Kuma tana kokarin hada hannu da gwamnati don samar da ingantaccen tsarin karatun Alkur’ani a ko’ina a Nijeriya
Tun a ranar asabar data gabata ne aka.fara wannan taron na kungiyar Huffazul.Qur’an ta kasa a Minna. Inda aka gudanar da saukar Alkur ‘ani da yawa a babban masallacin Juma’a na Minna.
Sannan Alarammomi da gwanayen karatun Alkur’ani suka yi musafa na Qur’ani a lokacin