HON MUSA NDAKPAYI NE YA DACE YA WAKILCI YANKIN CHANCHAGA
Daga Bala Musa Minna
An yi kira ga mutanen mazabar Chanchaga dake nan garin Minna anan Jihar Neja, dasu yi kokarin goyon bayan Hon Musa Usman Ndakpayi wanda shi ne ‘dan takarar Jam’iyyar APGA mai neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Chanchaga
Hon Musa Ndakpayi yayi wannan kiran ne lokacin dayake ganawa da manema labarai a wajen taron ganawa da mutanen Jihar.
Wanda da kungiyar matasa ta Nijeriya reshen Jihar Neja NYCN, Crusader Radio da kamfanin Jaridar NEWSLINE Newspaper suka shirya, a cibiyar yada al’adiu ta U.K. Bello dake nan Minna, ranar alhamis din nan data gabata
Inda ya ce ” gaskiya mutanen mazabar Chanchaga dake nan Minna babban birnin Jihar Neja suna bukatar wakilci ne na ‘dan siyasa mai amana da hangen nesa da neman ci gaban yankinsu
Shi yasa na amince in yi wannan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a wannan zaben dake tafe. Domin in wakilci mutanen Chanchaga. Saboda na dace da wannan matsayin , a cewarsa
Ya ce ” saboda a wannan yankin na Chanchaga aka haife ni kuma nayi makarantar Firamare da Sakandare anan. Kafin in wuce zuwa Jami’a don karo ilmi a fannin siyasa
Wannan ya nuna cewa ina da masaniya na abubuwan da mutanen Chanchaga sun bukata na inganta rayuwarsu. Sannan ina da manufar kawo canji na alheri ga mutanen wannan yankin
Ya kara da cewa ” garin Minna yana cikin karamar hukumar Chanchaga ne babban birnin Jihar Neja. Inda akwai mutanen kabilu daban-daban. Kamar Gwarawa, Nupawa, Hausawa, Yarbawa, Inyamurai da sauransu
Shi yasa nake ganin idan nayi nasara a zaben, zan yi kokarin ganin wadannan kabilu sun anfana daga wannan wakilcin da zan yi masu a Abuja. Wajen kawo masu ayyukan ci gaba
Ya ce ” kasancewar anan karamar hukumar Chanchaga nake zaune da mutane , zan yi duk abinda zai buniasa yankin, idan mutanen Chanchaga sum zabe ni a wannan matsayin”
Hon Musa ya bayyana cewa ina da shirye-shirye ( developmental programmes) a bangaren ilmi, kiwon lafiya, tsaro, kasuwanci,zamantakewa da sauransu
Wadanda idan Allah Ta’ala ta sanya na yi nasarar lashe zaben, zan yi anfani da kujerar wakilcin da zan yi mutanen Chanchaga wajen kawo masu ci gaba na harkokinsu
Shi yasa nake neman goyon bayan mutanen da suke da kishin karamar hukumar Chanchaga da Jihar Neja
Wajen ganin sun zabe ni karkashin Jam’iyyar APGA a wannan karon. Zan cika masu alkawari, a cewarsa