HUKUMAR NPC TA KASA TA NEMI GOYON BAYAN AL’UMMA WAJEN SHIRIN KIDAYAR YARA
Daga Bala Musa Minna
Hukumar kidayar al’umma ta kasa a Nijeriya NPC ta nemi al’ummar dake fadin jihar Neja da Nijeriya, dasu bayar da goyon bayan daya dace ga shirin kidayar yara kanana ( Child’s Birth Registration ) wanda hukumar zata fara gudanarwa a makon gobe
Shugaban hukumar kidayar na karamar hukumar Chanchaga dake jihar Neja Malam Lawal Tanko ne, ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki a harkar kidaya.
Wanda hukumar ta gudanar a sakatariyar karamar hukumar Chanchaga anan Minna, a jiya asabar
Inda ya ce ” hukumar kidaya ta kasa NPC ta horas da ma’aikatan da zasu gudanar da kidayar yara kanana masu shekara daya zuwa shekara biyar da haihuwa a yankin karamar hukumar Chanchaga da sauran kananan hukumomin jihar Neja a makon gobe
Domin sanin adadin yawan yara da ake haihuwa a kowace karamar hukuma. Saboda hakan zai taimakawa gwamnati wajen yin tsare-tsaren ayyukan ci gaban jama’a yadda ya kamata
Shugaban ya kara da cewa ” shi yasa muke kira ga sarakuna, ‘yan siyasa, shugabannin al’umma, iyaye da sauran jama’a, dasu baiwa ma’aikatanmu hadin kai. Wajen wayar da kan al’umma. Don samun nasarar da ake bukata
Shi ma Hon Yusuf Sulaiman wanda shi ne kansila mai wakiltar Nasarawa ‘A’ a karamar hukumar Chanchaga kuma wanda ya wakilci shugaban kansilolin karamar hukumarsa ya ce ” zamu tabbatar an samu goyon bayan da hukumar kidayar take bukata.
Domin zai taimakawa gwamnati wajen gudanar da ayyukanta na yau da kullum ga al’umma
Tun da farko dai, Hajiya Zainab Ayuba wacce ita ce shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA a karamar hukumar Chanchaga ta bayyana cewa, wannan shirin na kidayar yaran yana da muhimmanci sosai ga al’umma
Kuma zai tantance adadin yaran da ake haihuwa a kowane yanki na karamar hukumar da sauran wurare a fadin jihar Neja da Nijeriya.
A lokacin taron dai, an gayyato masu unguwanni, kungiyoyin nakasasau, malaman addini, ‘yan Jaridu da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kidaya. Saboda wayar da kan al’umma akan shirin