AN NEMI GWAMNATI TA SAMAR DA WURAREN KIWO DON MAGANCE RIKICIN MANOMA DA MAKIYAYA
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar alhazan jihar Neja Shaikh Abubakar Muhammad Rabi’u Beji ya nemi gwamnatin tarayya ta hanzarta samar da wuraren kiwo na zamani (grazing reserves) ga makiyaya. Domin magance rikice-rikicen dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya a Nijeriya
Shehin malamin yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu. Akan rikicin daya faru tsakanin manoma da makiyaya fulani a kauyen Barkuta dake kusa da garin Beji a karamar hukumar Bosso na jihar Neja, a makon jiya. Wanda ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi
Inda ya ce ” ya kamata gwamnatin tarayya dana jihohin kasar nan su hanzarta samar da wuraren kiwo na zamani (grazing reserves) a ko’ina cikin kasar nan. Saboda samun ingantaccen tsari na kiwo ga makiyaya. Ta yadda dabbobin makiyaya zasu samu wadatattun muhallin kiwo
Kuma manoma zasu rika noma kayayyakin gona a wadataccen wuraren noma. Ba tare da yin noma akan hanyoyin da dabbobi ko mutane suke zirga-zirga akansu ba
Ya kara da cewa ” Allah Ta’ala ya wadata Nijeriya da dazuzzukan masu yawan gaske wadanda har yanzu basu kare ba. Kuma har yanzu al’imma bata yin anfani dasu a kowane bangare
Ya dace gwamnati tayi anfani da wadannan dazuzzukan wajen ginawa makiyaya wuraren kiwo wadatattu. Domin samun kudaden shiga ga gwamnati da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma. Ta yadda za’a samu ci gaba mai inganci a bangaren kiwo da noma a Nijeriya
Sai kuma shugaban ya shawarci makiyaya da manoma wajen gujewa duk abubuwan da zasu rika kawo rikice-rikice tsakaninsu da juna.
Inda ya ce ” bayanai sun nuna cewa, asalin wannan rikicin daya faru na makon jiya a kauyen Barkuta, dabbobin wani ina makiyayi ne suka shiga gonar wani manomi suka yi masa barna. Wanda kuma a karshe rikici ya faru tsakanin makiyaya da manoma
Har ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi
Shi yasa nake kira ga manoma da makiyaya wadanda dukkaninsu suke anfani da dazuzzuka wajen yin sana’ar noma da kiwo, dasu rika kiyaye hakkokin juna zauna lafiya da juna
A karshe Shaikh Abubakar Beji ya yabawa kokarin gwamnatin Rt. Hon Umaru Muhammed Bago da mataimakinsa Kwamred Yakubu Garba. Wajen kokarin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Musamman wajen magance matsalolin rashin tsaro ko rikice-rikicen da suke faruwa a jihar. Ta hanyar anfani da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin zamantakewar al’umma