GWAMNATIN TARAYYA ZATA TALLAFAWA MUTANE MILIYAN 15 DON RAGE TALAUCI A NIJERIYA
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar bada tallafin kudade ga al’ummar Nijeriya Conditional Cash Transfer Office a jihar Neja Malam Sulaiman Husaini Kpange ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya zata baiwa al’ummar jihar Neja dana sauran jihohin Nijeriya tallafin kudade.
Domin rage radadin talauci da tsadar rayuwa dake damun al’umma sanadiyyar cire tallafin man fetur wanda gwamnatin Tinubu tayi tun a shekarar 2023
Shugaban hukumar yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake nan Minna, a yau alhamis
Inda ya ce ” a bana shekara ta 2024, gwamnatin tarayyar Nijeriya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo wani sabon shiri wanda a turance ake kira ( Renewed Hope Conditional Cash Transfer Programme )
Wanda gwamnatin tarayya zata baiwa mutane dubu darI biyu da goma sha tara da dari da ashirin da biyar ( 219,125 ) a jihar Neja tallafin kudade (grant)
Kuma wannan shirin na gwamnati zai anfanar da mutane miliyan goma sha biyar a sauran jihohin Nijeriya a wannan shekara ta 2024.
Ya ce ” gwamnati zata baiwa mutanen da sunayensu yake cikin rajistar gwamnatin tarayya na National Social Registar (NSR) da kuma rajistar Rapid Resond Rejister ( RRR ) tallafin naira dubu ashirin da biyar a kowane wata har zuwa watanni uku a jere
Za’a gudanar da wannan shirin ne a cikin watanni shida dake tafe a wannan shekarar a fadin kasar nan
Saboda ragewa mutane matsalar radadin talauci da tsadar rayuwar da suke fama da ita a halin yanzu, saboda cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya tayi
Ya kara da cewa anan jihar Neja, hukumar bada tallafin kudade ga al’umma na Conditional Cash Transfer (CCT ) ta gudanar da shirin tallafawa al’umnar jihar a shekaru bakwai da suka gabata
Inda suka rika baiwa mutanen da suka samu damar shiga shirin naira dubu goma a farkon shirin. Sai kuma hukumar ta bada naira dubu dari da hamsin ga wadanda suka samu damar shiga wannan shirin a karo na biyu ga talakawa
Saboda su rika gudanar da sana’o’i da kasuwancinsu domin dogaro da kansu. Domin magance matsalolin talauci da tsadar rayuwar dake damuwar al’umma a wurare daban-daban a cikin jihar Neja
A karshe Malam Sulaiman Husaini Kpange yayi kira ga al’ummar jihar dasu baiwa hukumarsa goyon bayan da take bukata. Ta yadda hukumar CCTO zata samu nasarar gudanar da ayyukanta ga al’umma