ANYI TARON KADDAMAR DA SHUGABANNIN KUNGIYAR HUFFAZU TA NEJA
Daga Bala Musa Minna
A yau Litinin ne aka gudanar da taron kaddamar da sabon zababben shugaban kungiyar Huffazul Qur’an da malaman addini ta kasa reshen jihar Neja Gwani Ambasada Husaini Abubakar Shakwata tare da sauran shugabannin kungiyar
An gudanar da taron ne a madarasatul Usshakun-Nabiy (SAW) dake bayan kamfanin Dana Pharmaceuticals Limited anan unguwar Maitumbi a Minna. Inda al’umma da yawa suka halarci taron
Anasa jawabin, sabon zababben shugaban kungiyar ta Huffazul- Qur’an da malaman addini ta kasa reshen jihar Neja Gwani Husaini Abubakar Shakwata yayi godiya ga Allah Ta’ala ne akan wannan amincewa na zabensa a matsayin shugaba da ‘ya’yan kungiyar suka yi
Sannan ya godewa gwamnatin jihar Neja karkashin shugabancin Rt. Hon Umaru Muhammed Bago wajen baiwa kungiyar gudumnawar da take bukata. Sai kuma yayi alkawarin gudanar da shugabanci na adalci wajen tafiyar da harkokin kungiyar
Domin samun hadin kan ‘ya’yan kungiyar da sauran al’umma. Saboda samun nasarar da kungiyar take bukata wajen ci gaban ta a jihar da Nijeriya gaba daya.
Sai kuma ya nemi goyon bayan ‘ya’yan kungiyar kodayaushe
Sai kuma Ambasada Gwani Musa Adamu Hadeja wanda shi ne shugaban kungiyar na jihohin tsakiyar arewacin Nijeriya ya bayyana farin cikinsa ne akan yadda kungiyar take kokarin kare martabar Alkur’ani mai Girma da almajiran dake karatun Alkur’ani a fadin jihar da Nijeriya
Shi ma Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida ( Cika-soron Minna ) wanda shi ne ya wakilci mai.martaba sarkin Minna Alhaji Farouq Bahago yayi ga al’umma ne wajen yin riko da koyarwar Alkur’ani mai Girma da hadisan Manzon Allah (S)
Saboda samun mafita daga matsalolin da jihar Neja da sauran kasashen duniya sukd fama dasu. Kamar matsalolin rashin tsaro talauci, lalacewar tarbiyar matasa da sauransu
Dayake nasa jawabin, ‘dan majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Chanchaga anan Minna, Hon Abubakar Abdullahi Buba ( Malam Cashier ) ya ce ” muna farin ciki da wannan kokari kungiyar Huffazul – Qur’an tayi na zaben mutanen da suka dace wajen shugabantar kungiyar
Sannan zan yi kokarin ganin na taimakawa kungiyar wajen ganin ta mallaki ofishinta domin samun damar gudanar da ayyukan ci gabanta ga al’ummar jihar Neja da Nijeriya. Muna yiwa kungiyar fatan alheri
Daga karshe an baiwa shugabannin kungiyar takardun shedar girmamawa da wasu manyan bakin da aka gayyata a taron. Saboda ayyukansu na samar da ci gaban kungiyar a fadin jihar Neja
An dai zabi Gwani Husaini Abubakar Shakwata da mataimakinsa Gwani Muhammad Salisu a matsayin mataimakinsa da sauran masu mukamai a kungiyar. Saboda tafiyar da shugabancin kungiyar a jihar don ci gabanta