TSARIN AIKIN HAJJIN DA GWAMNATIN SAUDIYYA TA KAWO A BANA ZAI SHAFI KASASHEN DUNIYA – NAHCON
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar alhazan Nijeriya NAHCON Alhaji Jalal Arabi ya bayyana cewa sabon tsarin da gwamnatin kasar Saudi Arebiya ta kawo wajen gudanar da ayyukan hajjin bana, zai shafi Nijeriya da sauran kasashen duniya
Shugaban yayi wannan kiran ne lokacin da kungiyar Jama’atu Nasril- Islam JNI ta gudanar da taronta na kasa. Wanda ta saba yi a kowace shekara. Taron ya gudana ne a garin Minna,,a makon jiya karkashin shugabancin mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar
Inda shugaban hukumar alhazan ya ce ” a bana shekara ta 2023 akwai damuwa sosai yadda gwamnatin Saudiyya ta zo da wani sabon salo na daban. Na takaita lokacin samun damar takardun shiga kasar Saudiyya ko biza ( Visa )
Saboda a shekarun baya, kasar Saudiyya ta kan bamu damar samun biza ( Visa) har zuwa kwana daya kafin tsayuwar arfa. Amma a bana Saudiyya ta sanya dokar rufe damar samun biza na zuwa aikin hajji tun daga kwanaki hamsin kafin tsayuwar arfa na bana
Wanda hakan yake nuna cewa akwai damuwa sosai ga al’ummar Nijeriya. Saboda yadda talakwan kasar nan suke fama da matsalolin tattalin arzikin Nijeriya a yanzu.
Shi yasa zamu yi kokarin tattara sunayen maniyyata da suka iya biyan kudaden aikin hajjin bana. Domin aikawa dasu kasar Saudiyya a karshen wannan wata na Disamba da muke ciki
Jalal Arabi ya kara da cewa ” a wannan tsarin da gwamnatin kasar Saudiyya ta kawo a bana na takaita kwanakin damar samun takardun shiga kasarta zai shafi Nijeriya da sauran kasashen duniya gaba daya ne
Shi yasa muke neman mai alfarma sarkin musulmi Sa’adu Abubakar da gwamnatocin Nijeriya tare da sauran shugabannin kasar nan su taimaka. Wajen hanzarta daukar matakan da zasu taimakawa hukumar alhazai ta Nijeriya da maniyyata aikin hajjin bana.
Saboda maniyyatan su samu damar cike sharudda ko ka’idojin da gwamnatin kasar Saudi Arebiya ta sanya a bana, wajen kammala biyan kudaden aikin hajji da sauransu, a karshen wannan wata na Disambar 2023. Saboda su tafi kasar Makkah don gudanar da aikin hajji idan lokaci yayi
Bugu da kari,a bana kasar Saudiyya ta sanya naira miliyan hudu da rabi a matsayin kudaden da kowane maniyyacin aikin hajji dake Nijeriya zai biya ga hukumar alhazai domin zuwa Makkah ya sauke faralin hajji yadda addini ya tanada
Dayake zantawa da wakilinmu, daraktan ayyukan hukumar alhazan jihar Neja Malam Attahiru Bala Dukku ya ce ” wannan lamari na aikin hajji bana ya zo da wani sabon tsari daga gwamnatin Saudiyya
Saboda haka muna kiran duk masu halin zuwa gudanar da aikin hajji suyi kokarin ganin sun biya kudadensu kafin lokacin ya wuce. Saboda yanayin da tattalin arzikin Nijeriya da na sauran wurare yake a fadin duniya yana shafar al’umma.
Sai dai muna ci gaba da neman gwamnati da sauran masu ruwa da tsakiyar a harkar gudanar da hajji a ko’ina, dasu yi kokarin taimakawa. Domin samun nasarar gudanar da aikin hajji a bana
Shi ma Alhaji Abu Sufyan Ahmad Siri-siri wanda shi ne Jami’in kula da alhazai na karamar hukumar Chanchaga kuma shugaban kungiyar jami’an kula da alhazai APWO’s forum na jihar Neja ya nemi maniyyata aikin hajjin da suyi kokarin biyan kudadensu na zuwa hajji kafin lokaci da gwamnatin Saudiyya ta sanya ya wuce
Sannan ya ce ” ina shawartar sauran mutanen dake bukatar zuwa aikin hajji a shekarar dake tafe na 2024, suyi kokarin tanadin biyan kudaden aikin hajji kafin lokaci ya wuce”
Jama’a dai suna kokawa da wannan sabon tsarin da gwamnatin Saudiyya ta sanya a bana wajen gudanar da wannan babban ibada na aikin hajji. Saboda zai shafi adadin maniyyata n da zasu iya biyan kudaden hajji a bana