JAMI’AN HUKUMAR KULA DA ABUBUWAN SUFURI NA V.I.O. A NEJA SUN KOKA
Daga Bala Musa Minna
Jami’an hukumar kula da sufurin motoci da sauran abubuwan sufuri ta jihar Neja NSMVAA ko V.I.O. sun yi kira ga gwamnatin jihar Neja karkashin Hon Umar Muhammad Bago. Wajen baiwa hukumar wadataccen kudade domin inganta ayyukan hukumar a fadin jihar
Shugaban sashen rajistar motoci na hukumar ta NSMAA Mr Steven Jiya wanda ya wakilci shugaban hukumar, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dake nan Minna, a makon jiya
Inda ya ce ” jami’an hukumar NSMAA ko V.IO. ta jihar Neja suna ayyukan binciken ingancin yanayin motoci da sauran abubuwan sufuri a fadin jihar. Domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka nan kuma hukumar tana sanya haraji ga direbobin motocin da suka yi laifuffukan da suka sabawa dokokin da hukumar ta sanya a wajen harkokin sufuri. Wajen hakan yake samar da kudaden shiga ga gwamnatin jihar domin samar da ci gaban jihar.
Amma gaskiya jami’an hukumar sukan fuskanci hatsari daban-daban saboda akan manyan hanyoyin motoci ne suke gudanar da wadannan ayyukan. Wadanda suna bukatar wadatattun kudade domin ingantasu
Shi yasa muke kira ga gwamnatin jihar ta yi kokarin baiwa hukumar kudaden da jami’anta zasu rika anfani dasu Wajen inganta ayyukan hukumar cikin sauki
Ya kara da cewa gwamnati ta samar da cibiyar kula da ingancin motocin hawa wato computerized vehicle inspection centre. Amma da yawan direbobi ko masu motocin hawa basu zuwa cibiyar domin a duba ingancin motocinsu.
Shi yasa muke ci gaba da daukar matakan wayar da kan direbobi. Saboda sanin muhimmancin zuwa wannan cibiyar.Ta yadda za’a duba duk wurare daban-daban na motar a gano inganci ko matsalolin da motar take dasu
A karshe Mr. Steven Jiya Kuma muna da jami’an hukumar a sauran kananan hukumomi guda ashirin da biyar na jihar. Wadanda suke gudanar da ayyukan hukumar ga al’umma. Saboda kiyaye dokokin tukin motoci, babura da sauran abubuwan hawa.