WAJIBI NE AL’UMMA SU RIKA GIRMAMA SAYYIDA FATIMATUZ-ZAHARA – Barista Buhari Yarima
Daga Bala Musa Minna
Shugaban jam’iyyar SDP na jihar Neja Baristar Buhari Yakubu Yarima (Makaman Chanchaga) ya bayyana cewa ya kamata al’umma su rika girmama matsayin ‘Nana Fatima ‘yar Manzon Allah (S). Domin kasancewarta abin koyi ga al’umma ne
Barista yayi wannan bayanin ne a wajen bukin mauludin Nana Fatimatuz-Zahara wanda ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky na Halkar Imam Hasan Al-Mujtaba suka gudanar a unguwar Chanchaga dake nan Minna,a jiya Talata
Ya ce “ya kamata al’umma su rika girmama matsayin Nana Fatimatuz-Zahara. Saboda ‘yar Manzon Allah ce fiyayyen halitta akan kowa. Sannan ita ce uwa ga muminai a wannan al’umma din.
Haka nan wajibi ne koyi da ita saboda Manzon Allah ne ya tarbiyyantar da ita. Kuma ya umurci al’umma suyi riko da koyarwarta dana sauran iyalan Annabi Muhammadu (S). Saboda samun tsira duniya da lahira
Ya dace al’umma su hada kai wajen gudanar da tarurrukan da zasu kawo hadin kai ga al’umma irin wannan taro da ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky suke gudanarwa kowane lokaci
A karshe Barista Buhari Yakubu Yarima yayi kira ga al’ummar Nijeeiya dasu yi riko da koyarwar Alkur’ani mai Girma da hadisan Manzon Allah (S).
Saboda samun mafita daga matsalolin rashin tsaro, talauci, lalacewar tarbiyyar da sauransu dake faruwa a cikin al’umma
A kowace shekara dai, ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da suke ko’ina sukan shirya tarurrukan tunawa da rayuwar Manzon Allah da Iyalan Gidansa tsarkaka a wurare daban-daban. Domin al’umma su yi koyi dasu