Gwamnatin jihar Neja zata samarwa dalibai motoci zuwa makaranta kyauta.
By Nura Mohammed
Gwamnatin jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya zata samarwa da dalibai motoci da zasu Rika daukan zuwa makaranta kyauta domin Kara karfafa zukatan su na zuwa makaranta a dukkanin fadin jihar don rage radadin cire tallafin Mai da gwamnatin taraya ta Yi.
Gwamna Umar Mohammed Bago shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakwancin Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO professor Dantani Ibrahim Wushishi a gidan gwamnati dake Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Gwamnan ya kuma bayana cewar Samar da motocin zai taimakawa dalibai a matakai daban daban ya Kuma karfafa masu kwarin gwiwar cigaba da Neman ilimi.
“Hakan da zamu yi zai rage radadin cire tallafin Mai da gwamnatin taraya ta Yi.” Inji Gwamna Umar Mohammed Bago.
Gwamnan ya kuma nuna bukatar ganin jihar Neja ta hada hannu da hukumar wajan ganin an magance matsalar rashin zuwa makaranta da wasu yaran a jihar musamman Yara mata, da Kuma yin anfani da ilimin na’ura Mai kwakwalwa na ICT a manhajar karatun jihar domin Samar da Cigaba a bangaran ilimi.
Har ila yau gwamna Umar Mohammed Bago ya ce akwai bukatar ganin hukumar ta NECO ta gudanar da ayyukan raya kasa ga alummar jahar ta yadda zata bada nata gudumuwar a kokarin gwamnatin na samarwa da alummar jihar ayyukan cigaba.
Gwamnan ya kuma bukaci hukumar ta NECO da ta kawo tsarin jarabawa na ayyukan hannu wato Vocational training a manhajar karatun makarantu domin taimakawa dalibai samun sana’oin da zasu dogara da shi.
Hakazalika Gwamna Umar Mohammed Bago ya kuma baiwa hukumar tabbacin gwamnatin sa na taimaka mata domin ta sami kwarin gwiwar cigaba da ayyukan ta kamar yadda yakamata.
” A matsayin mu na gwamnati mun nuna bacin ranmu na ganin hukumar bata yin yadda yakamata na ayyukan cigaban alumma, bamu ga ko bulo Daya da suka Gina aji ba da za a ce hukumar NECO ce ta Yi shi, ba za ku zama a jihar ba ku ki Samar da wani abun cigaba ga Yan jihar Neja ba.” Gwamna Umar Mohammed Bago.
” Hukumar NECO akwai bukatar ganin ta dauki nauyin gasar a makarantu kamar na karatu da rubuta da sauran su har ma da tsarin shiga azuzuwa domin a karantar da Yara kyauta.”
Gwamna Umar Mohammed Bago ya kuma koka kan yadda aka sami koma baya a jahar Neja a batun yiwa dalibai rijiatan jarabawa kammala karatun babban sakandare, inda nan take ya umurci sakataran gwamnatin jihar Neja Alhaji Abubakar Usman Gawu da ya duba batun.
Ya Kuma bayana kudirin gwamnatin na amincewa da kudi naira miliyan 30 a duk wata domin biyan bashin da hukumar ke bin gwamnati.
Tun da farko a jawabin sa Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO professor Dantani Ibrahim Wushishi ya ce makasudin ziyarar shine su taya Sabon Gwamnan murnar samun nasara a zaben da ya gudana.
Professor Dantani Wushishi ya Kuma bukaci hadin Kai daga Sabon Gwamnan domin ciyar da ilimi a jihar Neja gaba.
Ya Kara da cewar jihar Neja a baya ta sami nakasu wajan biyan kudin jarabawa ga daliban jihar tun daga shekarar 2018 har izuwa 2022.
A don haka Shugaban hukumar ya bukaci gwamnatin jihar Neja da ta himmatu wajan ganin ta Sanya yin jarabawar ga daliban jihar ya kasance dole ne, inda ya ce a shirye suka a bangaran hukumar su hada hannu da gwamnatin domin ciyar da ilimi gaba.