KUNGIYAR AYUPA TA YARBAWA TAYI TARON MURNAR NASARAR TINUBU DA BAGO
Daga Bala Musa Minna
Kungiyar hadin kai da ci gaban al’ummar Yarbawa mazauna arewacin Nijeriya wato Arewa Yoruba Unity & Progressive Association AYUPA reshen Jihar Neja, tayi taron nuna murnar zaben Bola Ahmed Tinubu shugaban kasar Nijeriya da Rt Hon Umar Muhammed Bago gwamnan Neja duk kansu na jam’iyyar APC
Inda ‘ya’yan kungiyar ta AYUPA suka fara da gudanar da tattaki daga Mobil Rounabout dake tsakiyar garin Minna zuwa sakatariyar jam’iyyar APC na Jihar Neja daura da Zarumai Primary. School anan Minna, a yau asabar da safe
Dayake jawabinsa a lokacin ziyarar , shugaban AYUPA ta Nijeriya Abdul-latif Aliyu ya bayyana cewa, sun gudanar da ziyarar ce don nuna farin cikinsu ga Allah Ta’ala daya baiwa Tinubu da Bago nasarar lashe zaben 2023.
Inda ya ce ” muna godewa jam’iyyar APC waxce ta zabi Tinubu da Bago a matsayin mutanen da suka cancanta su shugabanci al’umma a wannan karon.Muna godiya sosai akan hakan
Shi ma shugaban jam”iyyar APC na Jihar Neja Hon Halliru Zakari Jikantoro ya ce ” APC ta amince da Asiwaju Bola Tinubu don yafi kowane ‘dan siyasa samun mutanen daya kafa wadanda ‘yan siyasa ne a fadin Nijeriya. Kuma yana da farin jini
Muna fatan samun goyon bayan mutanen Neja dana Nijeriya saboda samun nasarar tafiyar da mulkin Tinubu da Bago a shekaru hudu masu zuwa
Haka nan kakakin jam’iyyar APC na Jihar Neja S.K Labaran ya ce ” Rt Hon Umar Bago yana da muradin sanya kowane bangare na al’umma a cikin .gwamnatinsa.
Shi yasa tun a yanzu wajen baiwa mutanen da gwamnan yake bukatar su yi aiki tare da shi, ya sanya AbdulHakeem.Abdurrahman wanda Bayarbe ne, ya kasance daya daga cikin mutane na farko da aka baiwa muka mu a gwamnatinsa.
Inda aka bashi mtasayin jami’i mai kula da harkokin cikin gida na musamman ga gwamnan Neja wato Specail Assistant on Domestic
A karshe shugaban kungiyar AYUPA reshen Jihar Neja Alhaji Jami’u Abdurrahman yayi godiya da fatan alheri ga mutanen Arewa yin kasar nan
Wadanda suka goyi bayan zaben Tinunu da Hon Bago. Kuma yayi fatan samun nasarar shugabancin jama’a da zasu yi