RANAR MA’AIKATA TA BANA: NLC TA NEMI GWAMNATI TA INGANTA YANAYIN MA’AIKATAN NEJA
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa a Nijeriya NLC reshen Jihar Neja Kwamred Abdulkareem Idrees Lafene yayi kira ga gwamnatin Jihar Neja data hanzarta samar da ingantaccen yanayin aiki ga duk ma’aikatan Jihar
Shugaban yayi wannan kiran ne a jiya litinin 1 ga watan Mayu na shekara ta 2023, wacce gwamnatin Nijeriya take sanyawa a matsayin ranar ma’aikatan kasar
A bana ma taron na ranar ma’aikatan ya gudana ne a filin wasa na 1-2-3 Quarters dake kusa da Old Secretariat, anan Minna
Inda dimbin kungiyoyin ma’aikatan gwamnati da kuma masu zaman kansu, tare da bangarorin gwamnati, sukan halarci taron.Don isar da kokensu ga gwamnati
A jawabinsa ga dimbin mahalarta, shugaban kungiyar kwadago ta NLC a Jihar Neja Kwamred Abdulkareem Lafene ya ce ” ma’aikatan Jihar suna matukar bukatar samun kulawar data dace daga gwamnati
Saboda hakan zai taimakawa ma’aikatan wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a ko’ina suke. Shi yasa taken ranar ma’aikatan bana shi ne : Neman ‘yanci ga ma’aikata.
Sannan ya dace ma’aikatan su tabbatar da suna gudanar da ayyukansu ga al’umma yadda ya dace idan sun gwamnanti ta inganta yana yin ayyukansu
Don a samu nasarar tafiyar da gwamnati bisa tsarin kundin mulkin Nijeriya.Yadda za’a bunkasa Jihar Neja a bangaren tattalin arziki da zamantakewar al’umma
Ya kara da cewa ” shi yasa na gabatar da koke-koken ma’aikatan Jihar Neja dana kananan hukumomi na Jihar ga gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello don ya baiwa ma’aikata hakkokinsu
Haka nan ya gabatar da wadannan koke-koken ga sabuwar gwamnatin Jihar wacce za’a rantsar ranar 29 ga wannan watan na Mayu shekara ta 2023 karkashin Rt. Hon Umar Bago. Don ta magance wadannan koke-koken ma’aikatan.
Daga cikinsu akwai neman biyan albashi bisa sabon tsarin da gwamnati ta amince. Biyan kudaden fansho da garatuti a lokacin daya dace.
Samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a ko’ina cikin Jihar ga al’umma. Sai biyan ma’aikata kudaden basussuka da alawus-alawus.
Sarmar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatan don su anfanar da al’umma. Haka nan NLC ta nemi gwamnati ta sake nazarin lamarin .korar wasu ma’aikatan jihae a shekarar 2021 da sauransu
Shi yasa kungiyar kwadago ta NLC tayi kira ga gwamnatin Rt. Hon.Umar Muhammed Bago data samar da kyakkyawan tsare-tsare don bunkasa harkokin ma’aikatan. Jihar
Haka nan shugabar ma’aikatan Jihar Hajiya Salamatu T. Abubakar wacce ta wakilci gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ta bayyana cewa , gwamnati tana sane da halin da ma’aikatan Jihar suke ciki
Kuma gwamnan Neja Alhaji Abubakar Sani Belli zai mikawa sabuwar gwamnati wadannan bukatu na ma’aikatan don a dauki matakan magance yadda ya dace
Shi ma shugaban kungiyar malamai ta NUT a Jihar Neja Kwamred Akayego Adamu Muhammed ya bayyana cewa, malaman makarantun boko sun fi damuwa akan rashin samun hakkokinsu daga gwamnati.
Amma zamu ci gaba xa baiwa sabuwar gwamnati shawarwarin da suka dace don magance matsalolin da ake fama da su
Shi.ma shugaban kungiyar ma’aikatan majalisar dokoki ta Nijeriya reshen Jihar Neja PASAN Kwamred Sanusi Salisu ya ce ” muna da koke-koke da yawa wanda muna fatan wannan sabuwar gwamnatin ta share mana hawaye akan su.
Muna baiwa sabuwar gwamnatin jihar Neja ta Hon Umar Muhammed Bago shawarar hada hannu da duk.masu nema ci gaban Jihar. Kuma muna yiwa al’umma fatan samun mafita na alheri a wannan karon
Sai dai a ranar ma’aikatan na bana, gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bdllo wanda wa’adin mulkinsa zai kare ranar 29 ga wannan wat an na Mayu 2923 bai zo wurin taron ba. Haka nan mataimakinsa da sakataren gwamnatin Jihar