YA DACE GWAMNATI TA DAMKA LAMARIN TAFIYAR DA MAKARANTUN ALLO A HANNUN WADANDA SUKA CANCANTA – Gwani Maiturare
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar Huffazul Our’an & Scholars Association of Nigeria reshen Jihar Neja Hafiz Ambasada Gwani Abukakar Sadik Maiturare yayi kira ga gwamnatocin Jihohi dana tarayyar Nijeriya, dasu rika damka harkokin tafiyar da makarantun allo a hannun mutanen da suka cancanta
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin daya zantawa da wakilinmu a jiya alhamis, a garin Minna na Jihar Neja
Inda ya ce ” ya dace gwamnatocin Jihohi dana tarayyar Nijeriya su rika baiwa mutanen da suka cancanta ragamar tafiyar da lamarin makarantu Allo a kasar nan
Saboda kokarin da gwamnatoci suke yi na samar da tsarin inganta makarantu. Allo yana samun cikas ne. Don rashin dacewar wadanda akan baiwa shugabancin abin lamarin
Ya ce ” gaskiya hanyar karatun Allo ne kadai sahihiyar hanyar da ake samun ingantaccen haddar Alkur’ani mai Girma
Shi yasa ya wajaba a rika baiwa ma’abota karatun Alkur’ani mai Girma na Allo wannan shugabancin ne. Saboda suna da kwarewa akan haka
Kamar ni da nake shugaban wannan kungiyar Huffazul Qur’an anan Jihar Neja, na yi shekaru 17 a makarantar Allo, har na rubuta Alkur’ani da kaina. Sannan na tafi kasar Sudan nayi karanci harshen Larabci.
Daga nan na dawo gida Nijeriya na yi karatu a Kano.Haka kuma nayi karatun Digiri a Jami’ar Abuja a harkokin addinin musulunci.
Kaga ina da kwarewar da ake nema wajen samar da ingantaccen tsari a wannan fagen. Kada a sanya siyasa wajen lamarin karatun Alkur’ani mai Girma. Domin akwai kwararrarun mutane da suka dace wajen rika tafiyar da karatun Allo
Muna shawartar gwamnati ta rika baiwa malaman dake karatun Allo shugabancin kulawa da makarantun Allo. Domin Zaka ga gwamnati ta baiwa wanda take so mukamin Director General na Tsangaya ko da basu cancanta ba
Amma a gaskiya sai kaga bai san komai a lamarin Tsagayu ba. Gwamnati takan bada wannan mukamin ga wanda yayi wa jam’iyyar gwamnati kamfe ne kawai
Bugu da kari ya ce ” wallahi duk yadda masu kokarin hana karatun Alkur’ani suke neman hana gudanar da shi ba zai yiwu ba. Wallahi wannan karatun Allo zai tabbata har abada, Sai dai a samar da hanyoyin inganta shi kawai.
Shi yasa aka kafa wannan kungiyar shekaru 24 da suka wuce na Nijeriya.
Kuma aka kafa ta anan Neja shekaru 8 da suka wuce.Don kare martabar karatun Alkur’ani mai Girma da Masu karatun Allo
Ya ce ” akwai hanyoyin magance barace-barace ga almajiran makarantun Allo. Sai kuma Iyaye su rika tallafawa makarantun Allo, Malamai su rika daukar almajiran da zasu iya kulawa dasu.
Sannan gwamnati ta rika baiwa makarantun Allo gagarumin Tallafi don su bunkasa
Wannan kungiyar ta samar da hanyoyin baiwa almajiran dake.karatun Allo Tallafin kudade na miliyoyin nairori don magance matsalar barace-barace na almajirai masu karatun Allo
Kamar yadda zamu sake bayar da Tallafin sana’o’i a makon gobe wajen taron da kungiyar Huffazul Qur’an & Scholars Association of Nigeria ta Kasa zata yi anan Minna dake Jihar Neja
Shi kuwa Alaramma Gwani Muhammadu Sani wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na kungiyar ya ce ” wannan kungiyar tana da almajirai ko. membobinta sama da dubu goma a Jihar
Sannan tana samar da hadin kan da ake bukata tsakanin almajiran cake karatun Alkur’ani mai Girma na Allo. Kuma tana tantance ayyukan ‘ya’yan kungiyar
Bugu da kari Alaramma Malam Salisu wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar ya ce ” wannan kungiyar tana taimakawa wajen samun kyakkyawan fahimta tsakaninta da gwamnati. Idan bukatar hakan ta taso
.Dayake magana akan lamarin kungiyar ta Huffazul Qur’an sakataren tsare-stare na kasa Alaramma Sadik M. I. ya ce ” kungiyar tana hada zamunci tsakanin ‘ya’yan wannan kungiyar .
Kuma gwamnatin tarayya tana anfani da wannan hadin kai tsakanin kungiyar da gwamnati wajen samun fahimtar juna
Kuma ya nemi duk ‘ya’yan kungiyar su kasance masu biyayya ga shugabannin kungiyar