GWAMNATIN BAGO TANA KOKARIN BUNKASA MA’AIKATAN KANANAN HUKUMOMIN NEJA NE – Hon Sidi Rijau
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi wato Local Government Service Commission na jihar Neja, Hon Isah Sidi Rijau ya bayyana cewa, gwamnan Neja manomi Rt. Hon Umar Muhammed Bago, yana kokarin bunkasa ayyukan ma’aikatan kananan hukumomi ne
Shugaban yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a jiya Talata, a ofishin hukumar dake Old Secretariat, anan Minna
Inda ya ce ” gwamnatin jihar Neja karkashin shugabancin Rt. Hon Umaru Muhammed Bago tana kokarin samar da matakan bunkasa bangaren ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar
Shi yasa muka ziyarci duk kananan hukumomin jihar da masarautu guda takwas dake jihar . Domin ganawa da ma’aikatan mu dake ko’ina a fadin jihar.
Inda muka zauna dasu sannan muka yi nazari akan nasaroriin da aka samu wadanda suka shafi ma’aikatan kananan hukumomi. Da samar da mafita akan matsalolin da suke janyo cikas a wannan bangaren
Ya kara da cewa ” ma’aikatan kananan hukumomi ne suka fi yawa a fadin jihar. Kuma suke da bukatar samun kulawan gwamnati. Shi yasa gwamnatin Umar Bago take kokarin samar da hanyoyin bunkasa ayyukansu
Haka nan, wannan hukuma dake kula da kananan hukumomin Neja, ta shirya taro ( seminar ) saboda horas da ma’aikatan da suka kusa barin aiki ko ritaya daga aikin gwamnati
Inda muka koyar dasu sana’o’i daban-daban kamar kiwon kaji, noma, kasuwanci da sauransu. Saboda su iya dogaro da kansu bayan sun bar aikin gwamnati
Sannan mun canzawa wasu manyan ma’aikatan kananan hukumomi kamar daraktoci kenan, wuraren ayyukansu. Da karin girma ga ma’aikatan a wuraren ayyukan su ( promotion exercise ). Da sauran wasu ayyukan da zasu anfanar dasu
Kuma muna taimakawa wajen daukar nauyin karatunsu a makarantu, idan sun samu damar shiga makarantun
A karshe Hon Isa Sidi ya nemi ma’aikatan kananan hukumomin jihar, su baiwa gwamnatin Rt. Hon Umaru Muhammed Bago goyon bayan daya dace. Saboda cimma nasarar da ake bukata a karkashin sabon tsari na NEW NIGER AGENDA