Daga Bala Musa Minna
An bayyana cewa gudanar da mauludin fiyayyen halitta Manzon Allah (S) yana janyo samun rahama da tsira a duniya da lahira a wajen Allah Ta’ala.
Wannan yana daga cikin jawabin da mai martaba sarkin Minna Alhaji (Dk) Umar Faruoq Bahago ya gabatar a wajen bukin mauludin Annabi Muhammad (S) na bana shekara ta 1446
Wanda ya saba shiryawa a kowace shekara. Wanda ya gudana a ranar lahadi, a fadarsa dake nan Minna
Inda ya ce ” hakika Manzon Allah (S) ya koyar da al’ummar duniya tarbiyya mai kyau ta hanyar gudanar da addinin musulunci yadda Allah mahalicci ya umurta a cikin Alkur’ani mai girma
Domin muyi koyi da rayuwar Annabi Muhammad dana Iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa na kwarai. Saboda mu samu rahamar Allah da da 1 tsira a duniya da lahira.
Da kuma samun mafita wajen magance matsalolin rashin tsaro, garkuwa da jama’a, talauci da sauran matsalolin da al’umma suke fama dasu a ko’ina
Shi yasa muke kiran al’umma wajen yin kokarin gudanar da bukukuwan mauludin fiyayyen halittu Manzon Allah (S) don akwai dimbin alheri mai yawa a cikinsa a duniya da lahira
Sannan sarkin ya jajantawa al’ummar masarautarsa wadanda suke fama da matsalolin rashin tsaro a yankunans. Inda ya nemi gwamnati ta taimakawa al’ummar masarautarsa dana sauran wuraren da suke fama da matsalar rashin tsaro. Wajen magance wannan babbar matsalar
Tun da farko dai, Na’ibin limamin babban masallacin Juma’a na Minna, Malam Isa Jibrin ya gabatar da nasiha ne bayan malamai sun kammala karanta litattafan yabon Annabi Muhammad da Iyalan gidansa tsarkaka, akan falalar girmama matsayin Manzon Allah (S).
Inda ya bayyana cewa, Allah Ta’ala yana bude kofofin alkhairansa masu yawa ga masu fifita darajojin Manzon Allah (S) akan sauran halittu
.
Haka nan Allah yana samar da aminci kwanciyar hankali da yalwar arziki ga al’umma albarkacin hidimtawa mauludin Manzon Allah (S)
A karshe malamin ya janyo hankalin iyaye da sauran al:umma wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu wajen nuna kauna ko soyayya ga Manzon Allahda Iyalan gidansa tsarkaka tare da riko da Alkur’ani mai girma