Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar tsare-tsaren biranen jihar Neja NUDB Hon Abdurrahman (JG ) Muhammad Chata yayi kira ga al’ummar jihar Neja, wajen nuna goyon bayansu ga ayyukan gwamnatin jihar karkashin shugabancin Rt. Hon Umaru Muhammed Bago
Shugaban yayi wannan kifan ne lokacin da yake zantawa da wakilimmu a ofishimsa dake harabar hukumar NUDB a tsohuwar sakatariyar jihar dake nan Minna
Inda ya ce ” an kafa wannan hukuma ta tsara birane na jihar Neja wanda a turance ake kira Niger State Urban Development Board (NUDB) ne domin samar da ingantaccen tsari wajen ci gaban al’ummar jihar.
Shi yasa gwamnatin jihar Neja karkashin shugabancin Rt. Hon Umar Muhammed Bago ta samar da sabon tsarin ci gaban jihar wanda ake kira NEW NIGER AGENDA
Ya kara da cewa ” a karkashin wannan sabon tsarin, gwamnatin Bago zata kawo sabbin tsare-tsare na zamani da ayyukan wadanda zasu anfanar da rayuwar al’umma
Hon Abdurrahman Chata ya ce ” wannan hukumar NUDB tana da kwararrun ma’aikata, amma babu wadatattun kayayyakin aikin da ma’aikatan hukumar suke bukata
Shi yasa muke kira ga gwamnatin manomi Bago, da ta yi kokarin samar da kayayyakin ayyuka na zamani wadatattu da kuma samar da kudaden alawus ( hazard allowances) da tsaro ga ma’aikatan hukumar. Domin muhimmantar da ayyukan da suke gudanarwa ga al’umma
Dayake amsa tambaya akan ko hukumar NUDB tana kokarin kulawa da tsare-tsaren gudaje ko muhallin al’umma da magance matsalolin da rashin ingancin na tsarin gina gidaje yake haifarwa a fadin jihar.
Kamar matsalar rushewar ginin bine (upstair) mai dauke da shagunan B.Y. Stores Ventures Nigeria Limited dake nan Minna a kwanakin baya
Sai shugaban hukumar ya ce ” a gaskiya muna daukar matakan da suka dace domin hana faruwar ire-iren wadannan matsalolin. Wadanda suke janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al’umma
Kuma hukumar NUDB ta rusa wannan ginin benen wanda mallakin wani ‘dan kasuwa ne dake anan Minna. Wanda wani bangare na ginin ya rushe. Wannan ya sanya hukumar NUDB ta rusa duk sauran ginin wannan benen daya rage.
Saboda ba shi da inganci ko karfin da zai iya daukar nauyin kayayyakin da kamfanin wannan ‘dan kasuwan ya sanya akan ginin na kayayyakin marmari ( soft drinks)
Inda a yanzu muka tilasta masa biyan haraji (penalty) akan sakacin da yayi na sanya kayayyakin da suka janyo rushewar ginin bene daya rufta akan jama’a. Wadanda da kyar aka ceto rayukansu.
Sannan muka tilastawa mai wannan kamfanin sake gina sabon muhallin ajiya (warehouse) na kayayyakinsa a wannan wurin daya rushe, amma bisa tsarin da hukumar NUDB ta samar. Kuma karkashin kulawar ma’aikatan mu. Wanda a yanzu aikin gina sabon wurin ajiyar kayayyakinsa yayi nisa sosai. Kaji halin da ake ciki yanzi kenan.
Ya ce ” ko a lamarin gina gidajen jama’a anan Minna da sauran wurare dake fadin jihar, muna hada hannu da ma’aikatar filaye ta jihar Neja ( Niger state ministry of lands) wajen samar da tsarin mallaka da gina gidaje ko muhallin zama ( residence ) yadda zai dace da al’umma wanda ba ahi da wata matsala. shi yasa muke daukar matakan
Shugaban hukumar ya bayyana cewa, muna anfani da kafafen yada labarai wajen wayar da ian al’ummar jihar a kowane lokaci. Domin sanar dasu muhimmancin tsare-tsaren hukumar kula da tsarin birane ta jihar Neja NUDB
A karshe Hon Abdurrahman Chata ya nemi al’ummar jihar Neja su baiwa gwamnatin Umaru Muhammed Bago goyon baya akan manufar NEW NIGER AGENDA don bunkasa jihar
Inda ya ce ” a yanzu gqamnatin Bago tana ayyukan gina hanyoyi a cikin garin Minna da unguwannin garin. Da bunkasa noma, gina asibitoci, makarantu a sauran wuraren da suke fadin jihar Neja domin anfanin al’umma. Shi yasa nake kiran jama’ar jihar, dasu baiwa gwamnatin Bago goyon baya don samun nasara