ALHAJI ABUBAKAR BOSSO YAYI KIRA GA SABBIN SHUGABANNIN NEJA
Daga Bala Musa Minna
Anyi kira ga sabbin shugabannin jihar Neja wadanda suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara ga gwamnati (special advisers) da manyan sakatarorin ma’aikatu (permanent secretaries) na jihar Neja dasu yi kokarin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar
Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Abubakar Yakubu Bosso (Mabudin Minna) wanda yayi bayan kammala taron rantsar da sabbin kwamishinoni da sauran masu mukamai a Neja
Wanda ya gudana a cibiyar Hon Justice Idris Legbo Kutigi Conference Hall, anan Minna, ranar litinin din nan
Inda ya ce ” ina kira ga wadannan sabbin shugabannin al’umma da gwamnan Neja Hon Umar Bago ya rantsar, suyi kokarin samar da hadin kai, zaman lafiya da bunkasa arzkin al’ummar jihar Neja
Saboda su kasance abin koyi ga sauran mutane a ciki da wajen jihar. Ta yadda al’umma ba zasu manta da ayyukan alherin da suka aikata ba
Kuma ya dace wadannan shugabanni su rika baiwa gwamnatin Umar Bago shawarwarin da suka dace a kowane lokaci. Ta yadda za’a samu damar bunkasa tattalin arzikin jihar yadda ya kamata
Bugu da kari,Alhaji Abubakar ya shawarci gwamnati ta tallafawa mata da matasa wajen koyar dasu sana’o’in da zasu rika anfanar kansu da al’umma
Ta yadda za’a magance matsalolin rashin ayyukan yi da talauci dake damuwar mata da matasa. Wanda hakan yake janyo suna aikata laifuffuka
Sai kuma yayi anfani da wannan damar a madadin masarautar Minna karkashin mai martaba Sarkin Minna Alhaji (Dk )Umar Farouq Bahago wajen godewa gwamnatin Jihar Neja karkashin shugabancin Hon Umar Muhammed Bago
Saboda baiwa ‘ya’yan masarautar Minna da sauran mutanen da suka dace wadannan mukamai. Don su wakilci jama’a yadda ya dace
A karshe Alhaji Abubakar Yakubu Bosso ya nemi sabbin shugabannin al’ummar karamar hukumar Bosso dana sauran kananan hukumomin jihar, dasu hada kansu tare da sauran mutanen yankunansu. Saboda tattauna hanyoyin samar da ci gaban su