SARKIN NOMAN MINNA YA MIKA TA’AZIYYARSA GA MATAIMAKIN GWAMNAN NEJA SABODA RASUWAR MATARSA
Daga Bala Musa Minna
Sarkin noman Minna Alhaji Danjuma wanda ‘dan uwa ne ga marigayiya Hajiya Zainab Garba uwargidan matiaimakin gwamnan Neja Kwamred Yakubu Garba, ya bayyana rasuwarta a matsayin rashi ne ga mutanen jihar
Alhaji Danjuma yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gidamsa dake Gbadanyi a unguwar Maitumbi, anan Minna, bayan rasuwarta, a jiya Talata 2/7/2024
Ya ce ” Ina mika ta’aziyyata dana iyalaina ga mijinta kuma mataimakin gwamnan Neja,, ‘yan uwanta da sauran al’umma, saboda rasuwarta. Domin ba karamin rashi ne gare mu ba da kuma sauran jama’a ba, inji shi
Saboda kyakkyawan halayenta na taimakon al’umma wadanda suka hada da maza da mata kowane lokaci suka bukaci hakan a wurin Hajiya Zainab
Ya kara da cewa ” Allah Ta’ala ne ya umurci al’umma wajen aikata wadannan halayen na kirki a cikin Alkur’ani mai Girma da hadisan Manzon Allah (S)
Shi yasa nake kira ga al’umma wajen yini koyi da halayen marigayiya Hajiya Zainab. Musamman mutanen suke da arziki a irin wannan lokacin da talakawa suke fama da matsalar tsadar rayuwa. Domin samun rahamar Allah Ta’ala anan duniya da lahira
Sannan yayi fatan Allah Ta’ala ya jikanta da rahamarsa. Ya sanya aljanna ce makomarta. Ya raya ‘ya’yanta data bar su da sauran danginta