AN KAFA HUKUMAR NSCHA DON TAIMAKAWA LAFIYAR AL’UMMA NE – Malagi
Daga Bala Musa Minna
Shugaban hukumar asusun taimakekeniyar kiwon lafiya ta jihar Neja wato Niger State Contributory Health Agency (NSCHA) Pharmacist Attahiru Shehu Malagi ya bayyana cewa gwamnati ta kafa wannan hukuma ce domin taimakawa al’umma musamman talakawan jihar
Shugaban hukumar yayi wannan bayanin ne lokacin ganawarsa da wakilinmu a ofishin hukumar dake Old Secretariat anan Minna, a yau Litinin
Inda ya ce ” wannan hukumar taimakekeniya ta kiwon lafiya zata saukakawa al’ummar jihar Neja a harkar kiwon lafiyarsu. Saboda an tanadar da tsari mai sauki da inganci ga al’umma wajen samun kulawar data dace a kiwon lafiya.
Ya ce ” muna baiwa al’ummar jihar tabbacin samun anfana daga shirin hukumar idan al’umma ta baiwa hukumar goyon bayan daya kamata. Ta hanyar yin rajista da hukumar yadda gwamnati ta tsara
Bugu da kari Malagi ya bayyana cewa ” mun ziyarci ma’aikatun gwamnati sarakuna, kungiyoyi, ‘yan Jaridu da sauran masu ruwa da tsari (stakeholders). Saboda wayar da kansu akan muhimmancin ayyukan hukumar ta NSCHA
Kuma a yanzu dai, muna kokarin ganin mun samu kyakkyawan fahimta da hadin kai daga gare su. Domin samun nasarar da muke nema akan shirin hukumar karkashin gwamnatin Muhammed Umar Bago a Neja
Shugaban ya ce ” kowane ma’aikacin gwamnati ( formal sector ) zai bada naira dubu uku da darI biyu ( N3,600) kowane wata wanda za’a rika cirewa daga albashinsa ne akan shirin. Yadda hakan zai anfanar da shi da iyalansa
Haka nan a bangaren kungiyoyi ko mutane dake zaman kansu ( informal sector ) kenan. Zasu rika bada naira dubu baiwa da dari biyu a shekara daya (N 7,200) . Ta yadda duk wanda yayi wannan rajistar da hukumar, zai anfana tare da ‘ya’yansu guda hudu
Ta yadda duk lokacin bukatar samun kulawa da lafiyarsu ya taso, hukumar zata tabbatar sun samu kulawar likitoci da magungunan da suka dace
Hukumar NSCHA ta sanya manyan cututtukan da suke damun al’umma musamman a jihar Neja kamar ciwon zazzabin cizon sauro (maleriya), ciwon asthma, tari, ulcer, hawan jini, kulawa da mata masu ciki da yin tiyata (surgery) ga mutanen da suke bukatar hakan da sauransu. Domin ceto rayywarsu daga salwanta
A karshe shugaban hukumar Pharmacist Attahiru Malagi ya nemi al’umma su baiwa hukumar goyon bayan daya kamata. Wajen anfana daga ayyukan
hukumar . Ta hanyar samun nasarar kulawa da lafiyarsu