WAJIBI NE KOYI DA MANZON ALLAH DON SAMUN TSIRA
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar Huffazul Kur’an ta kasa na jihohin tsakiyar arewacin Nijeriya Ambasada Musa Adamu Hadeja ya bayyana wajbcin koyi da fiyayyen halitta Manzon Allah (S) domin samun tsira duniya da lahira
Malamin yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala taron mauludin Manzon Allah (S).
Wanda shugaban kungiyar Huffazu na Neja Malam Husaini Abubakar Shakwata ya shirya a gidansa, dake unguwar Maitumbi anan Minna, ranar asabar data gabata. Yadda ya saba yi kowace shekara
Inda ya ce ” ya wajaba al’umnar musulmi suyi koyi da rayuwar Manzon Allah (S) a wajen kowane lamari na rayuwarsu. Saboda samun tsira a wajen Allah Ta’ala
Musamman a wannan halin da jihar Neja da Nijeriya tare da sauran kasashen duniya suke ciki a yanzu domin magance matsalolin da suke fuskanta
Shi ma shugaban kungiyar Huffazul Kur’an ta kasa reshen Jihar Neja Malam Husaini Abubakar Shakwata wanda shi ne ya shirya taron mauludin, ya ce ” wannan muhimmin taro ne domin girmama matsayin Manzon Allah (S) dana Iyalan gidansa tsarkaka
Kuma ya shawarci al’ummar musulmi dasu rika kokarin gudanar da ire-iren wannan taron. Saboda anfaninsa ga al’umma wajen fahimtar hakikanin rayuwar Manzon Allah (S)
Sannan yayi godiya ga malamai, manyan mutanen da aka gayyato da sauran wadanda suka halarci taron mauludin na Annabi (S).
A lokacin taron mauludin, malamai daban-daban sun gabatar da jawabai domin karantar da rayuwar Manzon Allah da yadda ya isar da sakon addini ga al’umma