MUNA KOKARIN BUNKASA KARATUN ALKUR’ANI NE – Husaini Shakwata
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar Huffazul Kur’an ta kasa reshen jihar Neja Malam Husaini Abubakar Shakwata ya bayyana cewa muhimmin abinda kungiyarsa ta sanya a gaba shi ne bunkasa yanayin karatun Alkur’ani mai Girma a jihar Neja da Nijeriya
Shugaban yayi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gidansa dake nan Minna, a makon jiya
Inda ya ce ” muna kokarin bunkasa yanayin karatun Alkur’ani ne domin samar da kyakkyawan yanayin ilmantar da almajiran dake karatun Alkur’ani a wurare daban-daban a Jihar.
Tare da koya da sana’o’i daban-daban gate su domin su iya dogaro da kansu a nan gaba. Wanda hakan zai magance matsalar barace-barace da sauransu
Bugu da kari kunhiyamu ta Huffazul Kur’an tana kira ga gwamnatin jihar Neja dana tarayya dasu hanzarta tallafawa kungiyar
Domin samar da ingantacciyar makarantar karatun Alkur’ani mai Girma wanda zata kunshi wajen koyar da sana’o’i ga almajirai musamman masu karatun allo.
Saboda a yanzu, makarantar Islamic Education Trust ( I.E.T ) na Shaikh Ahmed Lemu ce suke koyar da sana’o’i ga almajiran mu guda dari biyu sana’o’I
Shi yasa akwai bukatar mu mallaki namu cibiyar koyar da sana’o’i daban-daban ga almajiran mu. Domin samar da ingantacciyar makaranta da za’a rika karantar da al’umma Alkur’ani da sauran fannonin ilmi
Ya ce ” muna godiya ga gwamnatin jihar Neja karkashin Hon Umar Muhammed Bago da sauran masu tallafawa kungiyar domin gudummawar da suke bamu lokaci-lokaci
A karshe shugaban kungiyar yayi kira ga ‘ya’yan kungiyar. Inda ya ce ” muna nelihn.lman hadin kan membobin mu. Wajen baiwa kungiyar goyon bayan daya kamata. Wajen samun nasarar da ake nema