SARKIN MINNA YA NEMI MASU RIKE DA MUKAMAN SARAUTU SU SAMAR DA CI GABAN AL’UMMA
Daga Bala.Musa Minna
Mai martaba sarkin Minna Alhaji ( Dk) Umar Farouq Bahago ya nemi masu rike da mukaman sarautu a masarautar Minna, su yi kokarin samar da ci gaban al’umma. Musamnan a wannan lokacin da Nijeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki
Sarkin yayi wannan bayanin ne lokacin da al’ummar Yarbawa mazauna garin Minna suka kawo ziyarar godiya ga sarkin a fadarsa, ranar Litinin. Saboda nada ‘dan uwansu Alhaji Adekunle Abdulwaheed a matsayin Bangon Minna
Inda Alhaji Umar Farouq Bahago ya ce ” muna godiya ga Allah Ta’ala daya sanya muna da kyakkyawan alaka na zaman lafiya tsakanin mu da al’ummar Yarbawa dake wannan masarautar na tsawon
shekaru fiye da arba’in
Kuma muna anfanar da juna a harkokin zamantakewa na yau da kullum na al’umma a ciki da wajen jihar Neja. Wannan abin alfahari ne gare mu domin muna zaman girmama juna
Ya kara da cewa ” saboda haka ya kamata masu rike da sarautun gargajiya a wannan masarauta ta Minna suyi kokarin kawo ci gaban al’umma ta hanyoyin da suka dace don taimakawa jama’a
Dayake bayani akan matsayin sarautar Bangon Minna wanda Sarkin ya baiwa Alhaji Adekunle wanda Bayarbe ne mazaunin Minna, Mista Ajayi wanda jigo ne a cikin al’ummar Yarbawan Minna ya nuna farin cikinsa ne akan hakan
Inda ya ce ” muna matukar murna da godiya ga Allah Ta’ala daya sanya sarkin Minna ya rike Yarbawa tamkar ‘ya’yansa na jini. Wannan yana nuna amincewa da al’ummar Yarbawa ne a masarautar Minna da jihar Neja suka yi
Saboda tun zamanin sarkin Minna Alhaji Ahmadu Bahago yana raye yake yiwa al’ummar Yarbawa taimako a fannonin zamantakewa na yau da kullum. Kuma muna godiya da haka
Kuma al’ummar Yarbawa na wannan masarauta suna kokarin samar da shirin kawo masana’antu daban-daban a Minna don anfanar da al’umma
A karshe Alhaji Adekunle Abdulwaheed ( Bangon Minna ) yayi godiya ga mai martaba sarkin Minna da majalisarsa. Wajen nada shi a wannan mukamin don ya wakilci Yarbawa a majalisar sarkin Minna. Wajen bada gagarumar gudummawa ga ci gaban al’umma
Ya nemi Yarbawa da sauran mutane masarautar su ba shi goyon bayan daya dace tare da yi masa addu’a don samun nasarar aiwatar da ayyukansa ga al’umma yadda ya dace.