ZAN YI ADALCI WAJEN GUDANAR DA SHUGABANCI NA – Musa Nasko
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar kwadago na ma’aikatan hako ma’adinan kasa ta Nijeriya wato Nigerian Miners Workers Union reshen jihar Neja Alhaji Musa Adamu Nasko ya bayyana cewa zai gudanar da shugabancin kungiyar bisa adalci da rikon amana
Shugaban yayi wannan bayanin ne bayan sake zabensa a matsayin shugaban kungiyar a karo na biyu ta hanyar cancanta (concensus). Lokacin taron da kungiyar ta gudanar na wakilai na jihar ( state delegates conference ) karo na uku.
Wanda ya gudana a Dogon Koli Hotel Annex dake nan Minna, ranar asabar data gabata
Inda ya ce ” muna godiya ga Allah Ta’ala daya sake bamu damar shugabantar wannan kungiya ta ma’aikatan hako ma’adinai a jihar Neja.
Zamu ci gaba da neman ‘yanci ga ma’aikatan dake hako Ma’adinai a fadin jihar yadda dokar Nijeriya ta tanada. Saboda kawo ci gaban wannan babbar sana’a
Kuma a shirye muke wajen ci gaba da hada hannu da shugabannin kananan hukumomi da sauran hukumomin gwamnati wajen bunkasa harkokin hako ma’adinai a jihar
Shi ma shugaban kungiyar kwadago ta ma’aikatan hako ma’adinai ta Nijeriya kwamred Hamza Muhammed ya ce ” zamu ci gaba da kokarin tsabtace harkar hako ma’adinai da kare rayuka da mutuncin masu sana’ar hako ma’adinai wadanda sukayi rahista da wannan kungiyar
Haka nan Kwamishinan ma’aikatar harkokin ma’adinai a jihar Neja Hon Sabi Garba Yahaya ya ce ” gwamnati ta dakatar da ayuukan hako ma’adinai ne domin ta samar da kyakkyawan tsarin daya dace.
Saboda magance matsalolin tsaro dake faruwa ga masu wannan sana’ar. Musamman a wuraren da ake ayyukan hako ma’adinai. Ta yadda jihar Neja zata anfana a wannan bangare
A karshe Alhaji Usman Bello Paiko wanda yana daya daga cikin jigo a kungiyar ya bayyana cewa anyi wannan zaben ta hanyar cancanta (Consensus) ne domin membobin kungiyar sun aminta da shugabancin wadannan ‘ya’yan kungiyar