YA KAMATA AL’UMMA SUYI ANFANI DA BUKIN IDIL-FITIR WAJEN NEMAN RAHAMAR ALLAH – Nangau.
Sakataten karamar hukumar Bosso dake jihar Neja Hon ‘Danlami Mai Anguwa Nangau yayi kira ga al’ummar musulmi wadanda suke a karamar hukumarsa, da sauran wurare a ciki da wajen jihar Neja, dasu yi anfani da wannan lokacin bukin Idil-Fitir ko karamar sallah, wajen neman rahamar Allah da samar da zaman lafiya
Hon Danlami Nangau yayi wannan bayanin ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa dake garin Maikunkele hedikwatar karamar hukumar Bosso
Inda ya ce ” ya kamata al’ummar musulmin na karamar hukumar Bosso dana jihar tare da na sauran wurare a fadin duniya, su yi anfani da wannan muhimmin lokaci na Idil-Fitir wajen kyautata alaka tsakaninsu da juna
. Domin samun rahama daga Allah (SWT) da zaman lafiya a ko’ima. Tare da ci gaban arzikin al’umma
Haka nan kuma ya dace musulmi su ci gaba da yin riko da darussan da suka koya a watan azumin Ramadan wajen neman kusanci ga Allah. Ta hanyar gudanar da ayyukan alheri yadda Allah Ta’ala yake bada umurni a littafin Alkur’ani mai girma
Saboda samun mafita wajen magance matsalolin da suke damuwar al’umma a rayuwarsu na yau da kullum
Bugu da kari, sakataren ya nemi iyaye su muhimmantar da baiwa ‘ya’yansu tarbiyya yadda addinin musulunci ya koyar. Domin a samu matasan da zasu kasance masu anfani ga al’umma.
Inda ya ce ” wajibi ne iyaye su kasance masu kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu a kodayaushe. Kada a bari matasa su kasance masu aikata ayyukan ta’addanci ga jama’a
A karshe Hon ‘Danlami Nangau ya nemi al’umma
su ci gaba da nuna goyon bayansu ga gwamnan Neja Rt Hon Umaru Bago da shugabar karamar hukumar Bosso Hajiya Rakiya Ladidi Bawa Bosso. Domin samun ci gaban jihar gaba daya