YA KAMATA MASU ARZIKI SU RIKA ANFANI DA DUKIYARSU WAJEN CIYAR DA AL’UMMA
Daga Bala Musa Minna
An yi kira ga masu arziki ko mawadata dake a Nijeriya wajen rika anfani da dukiyarsu wajen ciyar da al’umma abinci. Musamman a wannan watan Ramadan mai tsarki.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Injiniya Aliyu Sakkwato wani ‘dan kasuwa dake nan garin Minna a jihar Neja. Lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Minna, a makon jiya
Inda ya ce” Allah Ta’ala ya kwadaitar da masu arziki ko wadata dake cikin wannan al’umma wajen ciyar da mutanen da suke talakawa.
Domin rage wa al’umma matsalar tsadar rayuwa da kuncin talaucin da suke fama da shi, sakamakon cire tallafin man fetur wanda gwamnatin Nijeriya karkashin shugaba Ahmed BolaTinubu tayi
Domin nuna tausayi da girmama al’ummar. Yadda hakan zai sanya farin ciki da cire masu damuwa da firgici a zuciyoynsu
Ya ce ” idan masu arziki sunantaimakon jama’a da dukiyarsu na halal, to! Allah Ta’ala zai sanya albarka da ci gaban arziki gare su yadda yayi alkawari a cikin Alkur’ani mai girma
Shi yasa nake kira ga duk masu arziki ko masu wadata, su rika ciyar da talakawa musulmi da Kirista a kowane lokaci. Saboda kowanensu halittun Allah ne. Wanda hakan yana janyo rahamarsa ga al’umma
Haka nan ya janyo hankalin al’ummar musulmi wajen kasancewa masu kokarin anfani da wannan wata na Ramadan wajen neman gafarar Allah ga kusanci gare shi.
Ta hanyar yawaita ayyukan alheri musamman na mu’amalar da suke yi na yau da kullum tsakaninsu da jama’a. Yadda Manzon Allah da Iyalan gidansa tsarkaka suka koyar da al’umma. Domin samun tsira duniya da lahira
A karshe Injiniya Aliyu Sakkwato yayi fatan al’ummar musulmi zasu yi anfani da darussan da suka koya a watan Ramadan na rikon amana, tausayi, ibada da sauransu ayyukan alheri wajen samar da kyakkyawan mu’amala tsakaninsu da al’umma
Inda ya ce ” addinin musulunci yana koyar da kyakkyawan tarbiyya ne ga musulmi. Ya kamata a rika ganin tasirin wannan tarbiyya da addinin musulunci yake koyarwa a gare mu. Saboda kiyaye mutuncin addinin a ko’ina