YA KAMATA AL’UMMA SUYI ANFANI DA BUKIN EASTER WAJEN ZAMAN LAFIYA – Nangau
Data Bala Musa Minna
Sakataten karamar hukumar Bosso dake jihar Neja Hon ‘Danlami Mai Anguwa Nangau yayi kira ga al’umma kiristoci da musulmin da suke karamar hukumarsa, da sauran wurare a ciki da wajen jihar Neja, dasu yi anfani da wannan lokacin bukin Easter wajen samar da zaman lafiya ga al’umma
Hon Danlami Nangau yayi wannan bayanin ne loka in da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa dake garin Maikunkele hedikwatar karamar hukumar Bosso
Inda ya ce ” ya kamata kiristoci da musulmin wannan yanki na Bosso dana sauran wurare a fadin jihar da Nijeeiya, su yi anfani da wannan muhimmin lokaci na Easter wajen kyautata alaka tsakaninsu da juna. Domin samun zaman lafiya da ci gaban arzikin al’umma
Haka nan kuma ya kamata musulmi suyi anfani da wannan azunmin watan Ramadan wajen neman kusanci ga Allah Ta’ala. Ta hanyar gudanar da ayyukan da suka dace yadda Allah Ta’ala yake bukata.
Saboda samun rahanarsa da magance matsalolin da suke damuwar al’umma a rayuwarsu na yau da kullum
A karshe Hon ‘Danlami Nangau ya nemi al’ummaasu ci gaba da nuna goyon bayansu ga gwamnan Neja Rt Hon Umaru Bago da shugabar karamar hukumar Bosso Hajiya Rakiya Ladidi Bawa Bosso. Domin samun ci gaban jihar gaba daya