An bude tafsir a Masalacin Hon Nma Kolo, an nemi masu mulki da suji tsoron Allah.
An kira ga shugabanni da su ji tsoron ranar haduwarsu da mahaliccin su kan yadda suka gudanar da shugabancinsu ga al’umma. Sheikh Muhammad Lawal Masha’Allahu ne ya yi kiran a lokacin da yake bude tafisirin Alkur’ani mai tsalki a masallacin gidan Jawon Minna, Alhaji Muhammad Nma Kolo a yammacin jiya daya ga watan Ramadan.
Shehin malamin ya cigaba da cewar tabbas shugabanni abin tambaya ne a gaban Allah bisa irin jagorancin da suka gudanar wa al’umma. Domin hadisin Manzon Allah ingantacce ya tabbatar shugabanni zasu zo ne a daure adalcin da su ka yiwa al’umma ne zai kwance su.
Saboda haka akwai bukatar kowani shugaba yayi bakin kokarinsa wajen sauke nauyin da ke kan sa, domin samun tsira ranar da nadama ba zai tai anfani ba.
Malamin, yayi tsokani mai tsawo game da Tauhidi, wato kadaita Allah, shi mika wuya tare da yadda da dukkanin kudura ta Allah, ta hanyar barin hada Allah da wani a wajen bauta, duba da yadda sauran halittu ke kaskantar da kan su saboda kaucewa fushin Allah.
Tafisirin, ya jawo hankalin al’umma wajen biyayya ga shugabanni, da hakuri da yanayi da yiwa shugabanni addu’a akan kurakurai tare da neman mafita ga Allah.
Masha’Allahu, ya jawo hankalin al’umma kan illar riko da wani abu sabanin Allah da irin talala da Allah ya yiwa masu shirka da shi. Duk yanayin da mutum ya samu kan shi da sanin Allah, saboda bai kamata kan wata jarabta ta rayuwa mutum ya rabu da imaninsa ba.
Malamin, yayi kira ga al’ummar musulmi da su yi anfani da wannan watan su yawaita karatun Alkur’ani mai tsaki, istigfari da taimakekeniya ga junan su musamman ganin irin halin da ake ciki na jarabawar imani.
O
A karshen bude tafisirin malamin ya jagotanci yiwa kasa da shugabanni addu’o’ da neman Allah ya yi riko da hannayen su akan daidai. Haka kuma yayi addu’ar shiya da neman zaman lafiya ga halin da kasar ke ciki na rashin tsaro.