RASUWAR GWANI ABUBAKAR BABBAN RASHI NE GA AL’UMMA- Farfesa N.Maiturare
Daga Bala Musa Minna
Tsohon shugaban jami’ar IBB University dake Lapai a Neja Farfesa Nasiru Maiturare ya bayyana rasuwar shugaban kungiyar Huffazul Qur’an & Islamic Scholars reshen Jihar Neja , Gwani Abubakar Sadik Maiturare a matsayin babban rashi ga al’umma
Farfesa Maiturare wanda ‘dan uwa ne ga marigayi Ambasada Gwani Abubakar Maiturare, ya bay ya na hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gidansa. Bayan kammala jana’izar marigayin a garin Paiko
Inda ya ce ” rasuwar Gwani Abubakar ya kasance babban rashi ne ga al’umma. Saboda yana kokarin ganin lamarin karatun Alkur’ani mai Girma ya inganta. Musamman wajen inganta karatun Alkur’ani na Tsangaya. Allah ya jikansa da rahama.Ya albarkaci iyalansa
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar Huffaz ta jihar Neja Alaramma Muhammad Salisu ya ce ” marigayi Gwani Abubakar ya samar da ci gaban kungiyar da hadin kan ‘ya’yan kungiyar. Muna fatan hadin kan ya ci gaba da dorewa
Ya samar da hanyoyin magance matsalar barace-baracen da almajiran masu karatun Allo suke yi a garuruwa manya da kanana a jihar Neja
Wanda hakan ya sanya kungiyar Huffazul Qur’an ta tallafawa wasu almajirai sama da biyu da kayayyakin sana’o’i daban-daban a fadin Jihar. Don samun hanyoyin iya dogaro da kansu
Haka nan sakataren tsare-tsare na kasa na cibiyar kula da karatun Alkur’ani mai Girma ta kasa Hafiz Sadik M.I. ya ce ” babban jarabawa ne ga kungiyar Huffazul.Qur’an ta Jihar Neja da Nijeriya. Muna rokon Allah Ta’ala ya jikansa da rahama
Shi dai, marigayi Ambasada Gwani Abubakar Sadik Maiturare ya rasu ne ranar laraba data gabata ne ya rasu. Bayan gajeruwar jinya da yayi fama da ita. Mutane daga wurare suna Nina damuwarsu akan rasuwar Gwani Abubakar don kyakkyawan halayensa na gari