IDIL-KABIR: SARKIN MINNA YAYI KIRA GA AL’UMMA WAJEN NEMAN RAHAMAR ALLAH
Daga Bala Musa Minna
Mai martaba sarkin Minna Alhaji (Dk) Umar Farouq Bahago yayi kira ga al’ummar musulmi dake ko’ina a Nijeriya da sauran kasashen duniya wajen anfani da lokacin Idil-Kabir ( babban salla) . Wajen neman rahamar Allah Ta’ala
Sarkin Minna yayi wannan kiran ne a sakonsa na taya al’ummar musulmi murnar bukin Idil- Kabir na bana. Wanda al’umma musulmi suke gudanarwa a kowace shekara, a watan Zhul-Hajjj
Wanda Allah (SWT) yake yiwa al’umma gafara da rahama a cikinsa. Kuma yake ‘yanta musulmi ta hanyar bude masu hanyoyin samun aljannarsa
Ya ce ” akwai dimbin falala da ayyukan alheri wadanda Allah Ta’ala yake bukatar kowane musulmi ya rika gudanarwa a kodayaushe. Musamman a wannan lokacin
Don samun rahama da tsira a duniya da lahira albarkacin Idil-Kabir . Wanda akanyi don koyi da Annabi Muhammad (S) da sauran Annabawan Allah wadanda suka koyar da al’umma tarbiyyar addini
Ya ce “saboda haka ya kamata musulmi su yi kokarin gudanar da addu’o’i na musamman a wannan lokacin. a masallatai, gidajensu, makarantu da wuraren haduwar jama’a
Don samun zaman lafiya da ci gaban masarautar Minna, Jihar Neja, kasar Nijeriya tare da sauran kasashen duniya musamman na musulmi don samun mafita daga halin kuncin da suke ciki
Har ila yau yayi kira ga iyaye da suyi kokarin baiwa ‘ya’yansu tarbiyyar data dace. Da sanya ido akan abubuwan da ‘ya’yansu ke aikatawa. Don su kasance masu anfani ga al’umma.
Haka.nan gwamnan Neja Umar Muhammed Bago wanda mataimakinsa Kwamred Yakubu Garba ya wakilta, ya nemi al’umma su rika aikata darussan da maiaman addini suke koyar da al’umma a kowane lokaci
.
Saboda samun kyakkyawan zamantakewa a tsakanin mutanen dake wannan al’umma. Da baiwa sabuwar gwamnatin Umar Bago goyon bayan da ya dace. Don samar da ci gaban Neja
A bana ma shekara ta 2023/1444, mai martaba. Sarkin Minna ya dakatar da hawan dawaki don yin zagaye a unguwannin garin Minna.
Yadda ya saba gudanarwa a masarautarsa lokacin bukukuwan Sallah karama Idil-Fitir da babbar Sallah Idil-Kabir ko babbar Sallah
Saboda jajantawa al’ummar da suke masarautarsa wadanda suke fama da matsalar rashin tsaro a yankunansu har yanzu. Wadanda ‘yan bindiga suke kashewa da yin garkuwa dasu