HUKUMAR ALHAZAN NEJA TA KAMMALA JIGILAR ALHAZAN JIHAR ZUWA MAKKAH
Daga Bala Musa Minna
A jiya alhamis 22 ga watan.Yunin shekara ta 2023, hukunar alhazan Jihar Neja karkashin shugabancin Ustaz Muhammad Awwal Aliyu Kwantagora tayi nasarar kwashe alhazan Jihar zuwa kasar Makkah. Don gudanar da ayyukan hajjin bana. Yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara
Yadda Hajiya Rukayyah Myhhamad Bawa shugaban sashen gudanar da harkokin hukumar alhazan Neja ta bayyanawa wakilinmu a sansanin alhazan Jihar dake nan Minna
Inda ta ce ” alhamdulillahi hukumar alhazan Neja ( NSPWB ) tayi nasarar jigilar duk alhazan Jihar guda dubu uku dari bakwai (3,700) na bana, zuwa kasar Makkah. Don yin ibadar aikin hajji yadda addinin musulunci ya tanada
Kuma mun yi anfani da jirgin FLY NAS na kasar Saudiyya wajen jigilar alhazan duk kananan hukumomin jihar guda ashirin da biyar cikin sauki akan lokacin da muka tsara.
Sai dai alhazan da suke fama da lalurar rashin lafiya ko mata masu juna biyu da sauransu. Wadanda na zasu iya gudanar da ayyukan hajji a bana ba
Sai Kuma matsalar jinkirin jigilar maniyyatan alhazan jihar ya faru ne saboda rashin samun takardun Visa daga hukumar shige da ficen Nijeriya yadda ya kamata. Don kadan-kadan muka rika samun takardun Visa din
Ta kara da cewa ” zamu kai duk koke-koke da rahotannin duk nasarori da muka samu a bana ga hukumar alhazan Nijeriya dake Abuja. Don magance su kafin gudanar da ayyukan hajjin na badi
Haka nan a wata takardar da hukumar alhazan jihar ta fitar ga manema labarai, shugaban hukumar alhazan jihar Neja Ustaz Muhammad Awwal Aliyu yayi kira ga alhazai su kasance masu aikata ibada a ki’ina yadda malaman addini suka koyar dasu. Saboda Allah Ta’ala ya karbi ayyukan hajjin da alhazai zasu gudanar a kasar Makkah
Sannan ya nemi duk alhazan jihar Neja su kasance masu bin doka da oda a kasar Saudiyya don kare mutuncinsu dana jihar Neja tare da Nijeriya a idanun duniya.
A bana shekara ta 2023, hukumar alhzan jihar Neja ta rika daukar alhazan jihar a motocin hukumar sufurin gwamnatin jihar na NSTA daga Minna zuwa filin.jirgin sama na Nnamdi Azikwe International Airport dake Abuja
Inda anan alhazan suke shiga jirgin saman da yake kaisu kasar Makkah don yin ibada. Saboda rashin kammala ayyukan gyare-gyare a filin jirgin sama na Minna.Wanda alhzan suka saba anfana da shi wajen jigilar su zuwa Makkah