NIJERIYA ZATA SAMU MAFITA DAGA MATSALOLIN DA TAKE FUSKANTA- Shugaban CAN na Neja
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar kiristocin Nijeriya (CAN ) reshen Jihar Neja Most Rabaran Dakta Bulus Dauwa Yohanna ya bayyana cewa Jihar Neja da kasar Nijeriya zasu samu mafita daga dimbin matsalolin da suke faruwa a cikinsu.
Wadanda suka hana ci gaban al’ummar dake zaune a cikinsu. Musamman a wannan lokacin da talakawa ke kokawa saboda yawaitar matsaloli
Shugaban yayi wannan bayanin ne a cikin sakonsa na lokacin bukin Easter. Wanda Kiristoci keyi a fadin duniya don koyi da sadaukarwar da Annabi Isa ko Yesu Almasihu yayi. Wajen isar da sakon Allah mahalicci lokacin rayuwarsa a duniya
Ya ce ” wannan lokacin na bukin Easter, wata dama ce ga kiristocin Jihar Neja da Nijeriya wajen neman kusanci ga Allah mahalicci.
Ta hanyar aikata ibada, addu’o’i ko ayyukan taimakon Jama’a da rike gaskiya. Yadda Annabi Isa ko Yesu Almasihu ‘dan Nana Maryam yayi lokacin rayuwarsa
Don samun mafita daga matsalolin da al’ummar Neja da Nijeriya suke fuskanta. Wadanda suka hada da rashin tsaro, lalacewar tattalin arziki, rashin ayyukan yi ga al’umma da sauran su.
Rabaran Bulus Dauwa wanda har ila yau
shi ne shugaban Cocin Katolika na yankin Kwantagora (Kontagora Diocese) dake Jihar Neja, ya ce ” Allah Ta’ala ya nemi duk Kiristoci dasu kasance masu kyakkyawar mu’amala tsakaninsu da sauran mutane
Shugaban Kiristocin na Neja ya godewa Allah mahalicci wanda ya sanya aka gudanar da zabubbukan gwamna dana ‘yan majalisun Jihar cikin kwanciyar hankali.
Sannan yayi fatan wadanda aka zaba a mukaman shugabancin siyasa a jihar, zasu yi kokarin sauke nauyin dake kansu na shugabantar al’umma yadda ya dace
Bugu da kari ya bayyana cewa ” muna yiwa duk al’ummar Neja da Nijeriya dake fama da matsaloli daban-daban a halin yanzu, addu’ar fatan alheri tare da samun mafita daga damuwar da suke ciki
Sannan muna jinjinawa jami’an tsaro dake kokarin magance matsalar rashin tsaro a wurare daban-daban a fadin Jihar Neja da Nijeriya.
Muna kira ga gwamnatocin Jihohi dana tarayyar Nijeriya, dasu hanzarta daukar matakan magance wannan matsala ta rashin tsaro . Da samar da kulawa ga iyalan wadanda suka sadaukar da rayuwarsu. Wajen samar da tsaro ga al’umnar Nijeriya