YA KAMATA GWAMNATI TA DAUKI MATAKAN MAGANCE MATSALAR ‘YAN DABA A MINNA – Ambasada Maiturare
Daga Bala Musa Minna
Anyi kira ga gwamnatin Jihar Neja karkashin shugabancin Alhaji Abubakar Sani Bello data gaggauta daukar matakan magance matsalar matasa masu harkar daba ko ‘yan sara-suka
Wadanda suke anfani da makamai wajen raunata mutane ko jikkatasu ko kisa.Tare da yin barnar dukiyoyin Jama’a da aikata sauran ayyukan ta’addanci a garin Minna
Wannan yana daga cikin bayanin da shugaban kungiyar Huffazul Qur’an & Scholars Association of Nigeria reshen juhar Neja Ambasada Gwani Abubakar Sadiq Maiturare yayi da wakilinmu
Lokacin daya ziyarci makarantar Malam Sulaiman Alaseni dake unguwar Daji anan Minna tare da tawagarsa, a ranar laraba data gabata
Don jajantawa wasu almajiran makarantar guda biyu, Tukur Muhammad da Muhammad Mustafa . Wadanda ‘yan Daba suka sassara da makamansu a ranar Juma’a data gabata
Ya ce ” wannan harin da ‘yan daba suka kaiwa wadannan almajiran abin takaici ne. Kuma abin damuwa sosai.
Wanda ya kamata gwamnati ta gaggauta daukar matakan da zasu magance wannan matsalar. Domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Minna
Tun da garin Minna yana da tarihin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya. Bai dace gwamnati ta bari a lalata wannan kyakkyawan tarihin ba
Wadannan almajirai da ‘yan daba suka sara, sun je debo ruwa ne a wata rijiya dake kusa da Skye Bank, anan unguwar Daji. Don ayi anfani da ruwan a wannan makarantar
Sai ‘yan Daba suka aukawa wadannan almajiran guda biyu da makamansu. Inda suka sassare su da raunatasu. Wanda hakan ya sanya suke jinya a yanzu haka
Ya kara da cewa “mun dade muna kaiwa gwamnati kokenmu akan matsalar wadannan matasa ‘yan daba da suke kaiwa jama’a hare-hare da makamai
Yanzu wannan babbar matasala tana shafarmu. Tun da ‘yan dabar nan suna sarar kowane mutum.ne har da almajiranmu. Sukan kai.hare-harensu a ko’ina
Yadda sukayi wa almajiran makarantar Malam Alaseni wadanda suke jinya a yanzu. Da sauran wasu almajirai a wasu wuraren da mutane da suke kasuwanci ko sana’o’insu
Kuma ko a kwanakin baya, sun kashe wani almajirin Malam Basiru dake unguwar Limawa anan Minna da sauran wasu mutanen tare da lalata dukyoyi ko sace su.
Ambasada Maiturare ya ce ” mun dade
muna bada shawara ga gwamnati akan daukar matakan da zasu magance wannan matsalar lalacewar matasan da suke harkar daba ko ‘yan sara-suka.Amma har yanzu dai, lamarin yana nan
Saboda dayawan wadannan matasan dake harkar daba ko.sara-suka basu da ayyukan yi. Suna zama ne kawai
Basu samu tarbiyyar makarantar addini ko na Boko ba
Shi yasa halayensu ko ‘dabi’unsu ya lalace. Sai suke anfani da wukake, adda, gariyo da sauran maiamai wajen kaiwa mutane hare-hare a. gidajensu, kasuwanni,makarantu, unguwanni da sauran wuraren zaman jama’a
Wannan ya sanya muke kiran gwamnati ta dauki duk matakan da duk dace wajen magance wannan lamarin. Domin a samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma