HON UMAR BAGO YA DAUKI NAUYIN SAMAR DA KIWON LAFIYA GA MUTANE NEJA – Dr Mustafa Alheri
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kwamitin kiwon lafiya na ‘dan takarar gwamnan Neja na APC Dakta Mustafa Jibrin Alheri ya bayyana cewa dan takarar gwamnan Neja na Jam’iyyar APC Rt Hon Umar Muhammed Bago ya dauki nauyin samar da shirin kulawa da lafiyar Jama’ar Neja kyauta
Dakta Mistafa yayi wannan bayanin ne ga manema labarai a fadar mai martaba sarkin Minna Alhaji (Dk) Umar Farouq Bahago, a makon jiya.
Inda likitoci suka rika duba mutanen da basu da lafiya ko suke bukatar samun magunguna. Kuma an samu dubban mutanen masu matsalolin rashin lafiya daban-daban da suka halarci wurin da akayi taron
Wadanda suka zo wannan program domin neman lafiyar jikinsu. Kuma likitoci sun duba lafiyarsu. An basu magunguna kyauta. Sannan wasu mutanen anyi masu aikin fitar da cututtukan jikinsu (surgery) kyauta
Wannan abin yabawa ne musammaan a wannan lokacin da mutane da yawa basu da kudaden da zasu iya sayen magunguna ko samun likitocin da zasu duba lafiyarsu
Dakta Mustafa ya kara da cewa ” a yanzu likitoci duba mutane marasa lafya a wannan yanki na gabashin Jihar Neja. (Zone B) kenan fiye da mutane dubu biyar.
Haka nan a sauran yankunan Jihar wato Zone A da zone C. Inda aka samu nasarar gudanar da wadannan ayyukan kiwon lafiya ga mutanen da suke bukatar kulawar lafiyarsu
Wanda a karshen wannan shirin, mutane fiye da dubu goma sha biyar me zaau anfana sosai daga wannan shirin kulawa da lafiyar al’umma kyauta na ‘dan takarar gwamnan Neja Rt. Hon Umar Muhammed Bago
A karshe Dakta Musrafa Jibrin ya nemi mutanen Jihar Neja su zabi Hon Umar Bago a wannan zaben dake tafe domin ci gaba da samun ayyukan bunkasa rayuwar al’umma