YA KAMATA AL’UMMAR NEJA SU ZABI MUTANEN DA SUKA CANCANTA NE
Daga Bala Musa Minna
Shugaban kungiyar Huffazul Qur’an & Scholars na Jihar Neja Ambasada Gwani Abubakar Sadik Maiiturare yayi kira ga al’ummar Jihar Neja dana sauran wurare a Nijeriya, da suyi sun kokarin zaben shugabannin da suka cancanta wajen gudanar da harkokin mulki
Shugaban yayi wannan kiran ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa dake nan Minna, ranar Juma’a data gabata
Inda ya ce ” ina kira ga al’ummar Jihar Neja da sauran mutanen Nijeriya, dasu zabi mutanen da suka cancanta masu rikon amana. Wadanda zasu shugabanci mutane a mukaman siyasa a daban-daban
Saboda samun kwanciyar hankali da zaman lafiya da magance matsalar rashin tsaro. Tare da samun mafita a sauran abubuwan da suke damun al’ummar Jihar Neja da Nijeriya
Domin a yanzu kowa yana ganin halin da Nijeriya take ciki. Inda al’ummar kasar suke kokawa akan yadda gwamnati take tafiyar da harkiokin shugabanci ga Jama’a da suka zabi wannan gwamnatin ta APC
Shi yasa nake kiran kowane ‘dan Nijeriya yayi kokarin mallakar katun Jefa kuri’arsa wato Permanent Voters Card. Don ya zabi shugaban da zai karewa al’umma mutuncinsu. Kuma ya kiyaye hakkin addini ga Jama’a
Haka nan Gwani Abubakar Maiturare yayi kira ga gwamnati data baiwa masu karatun Qur’ani mai Girma dake makarantun Tsangaya, gudummawar data dace don bunkasa karatun Alkur’ani a kasar
Inda ya ce ” ce ” kwanan nan kungiyar Huffazul Qur’an tayi taronta na kasa a nan Minna. Inda Alarammomi daga Jihohin talatin da uku suka halarci taron.
Anan muka gudanar da addu’o’i na musamman akan matsalar ‘yan bindiga da kuma zaben dake tafe a Nijeriya. Tare da tattauna yadda za’a inganta tsarin karatun Alkur’ani na Allo a tsarin Tsangaya a kasar nan
Shi yasa nake ci gaba da kiran a
Alarammomi da malamai tare da sauran mutane a Jihar Neja da sauran wurare a kasar nan, dasu ci gaba da addu’ar neman zaman lafiya a fadin Nijeriya
Musamman lokacin wadannan zabubbukan da suka tafe nan da wasu ‘yan kwanaki a Nijeriya. Tare da kiran iyaye dasu rika yiwa ‘ya’yansu tarbiyyar data dace. Domin su kasance matasa masu anfanar da al’umma