HAjj 2023: Jirgin farko na Alhazan jihar Neja ya sauka filin jirgin saman Abuja.
Tawagar farko na alhazan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya su 410 sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 2:35 agogon Najeriya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar jin dadin alhazan jihar Neja Hassan Danladi Idiris ya fitar ya bayana cewar hukumar jin dadin alhazan jihar ta nuna gamsuwar ta bisa yadda aka sami nasarar tsarawa da kuma shirya kwaso alhazan bisa jaddawalin hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta tsara.
Tun dai da misalin karfe 10 na safiyar talatan na agogon saudiya jirgin kamfanin jirgin flynass Air ya kwaso alhazan zuwa Najeriya bayan kammala dukkanin shirye shirye bisa tsarin hukumar NAHCON ta kasa.
Hassan Danladi Idiris ya Kuma kara da cewar hukumar jin dadin alhazan jihar zata Kara himma wajan ganin sauran alhazan sun sami isowa gida Najeriya kamar yadda aka tsara.
Alhazan jihar Neja su 3700 ne suka sami damar sauke farali a wannan shekarar da muke ciki na 2023. Inda ake saran kwaso sauran alhazan da yanzun haka suke kasa Mai tsarki.