HUKUMAR ALHAZAN NEJA TA FARA KWASHE ALHAZAI 3,709 ZUWA KASAR MAKKAH
Daga Bala Musa Minna
A jiya juma’a 9 ga watan Yuni na shekarar 2023 ne , hukumar kula da alhazan Jihar Neja karkashin shugabancin Ustaz Muhammad Awwal ta fara jigilar alhazan Jihar zuwa kasar Makkah (Saudi-Arebiya) . Don gudanar da ayyukan hajjin bana
Kuma a bana gwamnatin Jihar karkashin shugabancin Rt Hon Umar Bago ta sanya mai martaba Sarkin Borgu Barista Muhammad Sani ‘Dantoro Kitoro (IV) a matsayin Amirul Hajj na Jihar Neja
Dayake jawabinsa ga alhazan Neja a filin jurgin sama na Abuja Hon. Yakubu Garba wanda shi ne mataimakin gwamnan Neja Umar Bago yayi nasiha ne gare su don kiyaye dokokin kasar Saudiyya
Inda ya ce ” muna fatan alhazan Neja zasu kasance masuu kulawa da ayyukan hannun da suka je gudanarwa yadda addini ya tanadar. Sannan su kiyaye dokokin kasar Saudiyyah.
A zantawarsa da manema labarai a sansanin alhazan Jihar dake unguwar Tudun Fulani anan garin Minna, shugaban sashen jigilar alhazan Jihar Malam Attahiru Bala Dukku ya bayyana yadda lamarin yake
Inda ya ce ” a bana Jihar Neja tana da alhazai ko maniyyta aiki hajji guda dubu uku da dari bakwai da tara (3,709 ).
Kuma mun fara jigilar wadannan alhazan zuwa filin jirgin sama na Abuja. Don kaisu kasar Makkah ( Saudi- Arebiya ) yadda aka saba duk shekara Inda zasu gudanar da ayyukan hajji yadda addini ya tanadar
A bana muna anfani gayyato kamfanin jiragen sama na FLY NAS mallakar kasar Saudiyya. Don jigiilar alhazan Jihar Neja zuwa Makkah kafin lokacin da gwamnatin kasar Saudiyya ta sanyawa Jihar
Haka nan shugaban kwamitin kula da harkokin alhazai na majalisar dokokin Jihar Neja kuma ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Mashegu Hon Abubakar Umar ya ce ” muna godiya ga Allah Ta’ala daya bamu ikon gudanar da shirye-shiryen ayyukan hajji na bana cikin nasara
Hon Sulaiman Gambo Rabi’u mataimakin shugaban kwamitin alhazai na majalisar dokokin Neja kuma ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Paikoro ya ce “gwamnatin Jihar Neja karkashin Umar Muhammed Bago ta samar da motocin da zasu dauki alhazan Jihar daga nan Minna zuwa filin jirgin sama na Abuja. Inda za’a kwashe su zuwa kasar Makkah don yin ayyukan hajji
Hon Umar Jibrin Igade shugaban karamar hukumar Mashegu dake Jihar Neja ya ce ” abin farin ciki ne kowane shekara alhazan Mashegu ne na farko wajen zuwa kasar Makkah a Neja.
Muna fatan alhazanmu zasu roki Allah Ta’ala ya magance mana matsalolin dake damun al’umma. Musamman matsalar rashin tsaro dake faruwa a Mashegu, Jihar Neja da Nijeriya.
Muna kira ga alhazai karamar hukumar Mashegu dana Neja tare da sauran alhazan Nijeriya, su kasance masu bin dokokin kasar Saudiyya. Don kiyaye mutuncin Nijeriya a ko’ina
Tun a bara shekara ta 2022 dai, gwamnati tana daukar alhazan Jihar Neja ne a motoci daga sansaninsu dake nan garin Minna zuwa filin jirgin sama na Abuja. Saboda tafiya kasar Makkah maimakon anfani da filin jirgin sama.na Minna.
Inda gwamnati Jihar Neja ta bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ayyukan gyare-gyraren da gwamnat take ci gaba da gudanarwa a filin jirgin sama na Minna a shekarun nan suka janyo hakan