AMBASADA NURA HASHIMU YAYI KIRA GA AL’UMMA DASU ZABI PDP. A NEJA
Daga Bala Musa Minna
Hon Ambasada Nura Hashimu (Tallafin Bosso Karami) kuma darakta na yakin neman zaben ‘dan takarar kujerar Sanata Hon Isyaku Ibrahim SAN na karamar hukumar Bosso na. Jihar Neja, ya nemi al’ummar yankinsa da Jihar Neja, dasu zabi duk ‘yan takarar PDP a zaben dake tafe na bana shekarar 2023
Hon Nura yayi wannan bayanin ne lokacin ganawarsa da manema labarai a ranar asabar data gabata.
Lokacin taron da shugabannin Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bosso suka shirya. Don wayar da kan al’ummar Fulani dake wurare daban-daban a Jihar akan zaben dake tafe
Inda ya ce ” mun shirya wannan taron ne don wayar da kan al’ummar Fulanin Neja da sauran mutane. Don su zabi Jam’iyyar PDP, lokacin zaben 2023 dake tafe nan da wasu ‘yan kwanaki
Saboda samun mafita don magance matsalolin talauci, rashin ayyukan ci gaban al’ummar Jihar. Tare da magance rashin tsaro dake janyo hasarar rayuka da dukiyoyin mutane a garuruwa da kauyuka a ciki da wajen Jihar Neja
Shi yasa muke kokarin wayar da kan al’ummar Fulani da sauran masu goyon bayan PDP. Da tsayawa wajen kare kuri’unmu a zaben. Don tabbatar da nasarar da muke da kyakkyawan fatan samu a wannan zaben
Sannan Hon Nura Hashimu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga al’ummar Fulani wadanda suke fama da hare-haren ‘yan bindiga a ciki da wajen Jihar
Shi kuwa shugaban Fulani Forum na Jihar Neja masu goyon bayan Jam’iyyar PDP, Aliyu Umar ya ce ” mun yi wannan taro ne don tunatar da Fulani yadda matsalar rashin tsaro ya shafi Fulani
Sannan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali wajen lamarin zamantakewa na yau da kullum tsakanin Fulani da kowace kabila.
Musamman tsakanin manoma da Fulani makiyaya a wurare daban-daban. Saboda samun ci gaban arziki da kwanciyar hankali
Shi kuwa shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bosso Hon Umar Garatu yasa muke neman Fulanin Jihar Neja dasu goyi bayan Jam’iyyar PDP a wannan zaben dake tafe na bana. Domin a samu gwamnatin da zata baiwa Fulani kyakkyawan kulawar data dace
A karshe shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bosso Hon Danlami Aliyu Sabon- Daga ya nemi al’umma su hada kansu ne lokacin zabubbukan da suke tafe. Domin su zabi PDP a kowane matakin na mukaman siyasa