KU ZABI ATIKU NA PDP DON CI GABAN NIJERIYA – Sani Shu’aibu
Daga Bala Musa Minna
Anyi kira ga ‘yan Nijeriya dasu zabi Alhaji Atiku Abubakar ( Wazirin Adamawa ) ‘dan takarar kujerar shugabancin kasar nan na Jam’iyyar PDP a zaben dake tafe ranar 25 ga watan Fabrairun bana
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Alhaji Sani Shu’aibu mai Gold shugaban kungiyar Nigerlites Marketers Concern Forum na Jihar Neja, a ofishin kungiyar dake Gamji Plaza, daura da babbar kasuwar Engr A.A.Kure na Minna, lokacin daya zanta da wakilinmu, ranar Laraba
Inda ya ce ” muna kira ga mutanen Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya, dasu zabi Alhaji Abubakar Atiku ‘dan takarar shugabancin kasar nan na Jam’iyyar PDP a wannan zabe na bana
Don samar da shugaban kasar da zai kawo ayyukan ci gaban al’umma a Nijeriya. Kuma ya fitar da al’ummar kasar daga matsalolin talauci, rashin tsaro da sauran matsalolin dake damun Jama’a
Ya kara da cewa ” lokacin mulkin PDP na shekaru 16, Atiku yayi kokari wajen kawo ci gaban harkokin kasuwanci da zamantakewar mutanen kasar nan.
Wannan yana daya daga cikin ayyukansa
Hakan ya nuna cewa ko a yanzu idan aka zabe shi, zai kawo ci gaban Jihar Neja da Nijeriya. Yadda yayi alkawarin kammala aikin gina mashigin ruwa na Baro dake nan Jihar Neja
Bugu da kari, Alhaji Sani Shu’aibu ya ce ” wani abin farin ciki ne shi ne yadda zuwan Atiku da tawagarsa garin Minna a makon jiya don.kaddamar.da yakin neman zabensa da sauran ‘yan takarar PDP na Neja
Wannan taron ya girgiza kowa sosai. Domin kowa yaga yadda mutanen Neja sukau yi masa tarbo na girmamawa da nuna aniyarsu na zaben Atiku
Inda dimbin magoya bayan PDP suka nuna kauna gare shi. Ta hanyar nuna masa goyon bayanoa yanzu mutanen Nijeriya suna kukan halin kunci da takarar da gwamnatin APC karkashin shugaba Buhari ta jefa al’umma a ciki.
Wannan ya janyo mutane suke ta neman Atiku ya shugabanci kasar nan.Saboda zai ci gaba da samar da hanyoyin inganta rayuwar mutane
Musamman ‘yan kasuwa, manoma, ma’aikatan gwamnati da sauransu, zasu anfana matuka daga gwamnatin PDP idan an zabe ta a bana..
yaga yadda mutane suka yi maraba da Atiku anan Minna da sauran Jihohin daya i mai kyau
A karshe Alhaji Sani Shu’aibu mai Gold ya nemi kowa ‘dan Nijeriya daya hanzarta samun katin zabensa na PVC. Sabida samun damar zaben PDP a duk zabubbukan dake tafe a bana